An sallami wani ma’aikacin gwamnati saboda goyon bayan jam’iyyar APC a bayyane

An sallami wani ma’aikacin gwamnati saboda goyon bayan jam’iyyar APC a bayyane

Kamfanin jiragen sama na Ibom Air mallakin gwamnatin jahar Akwa Ibom ta sallami wani ma’aikacinta mai suna Daniel Utomette sakamakon bayyana goyon bayansa a fili ga jam’iyyar APC, jam’iyya mai mulki a matakin kasar Najeriya, amma kuma jam’iyyar adawa a jahar Akwa Ibom.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar 9 ga watan Mayu ne kamfanin ta sallami Daniel, bayan daukansa aiki da kwanaki bakwai a matsayin mai kula da sashin girke girje da tande tande na kamfanin jirgin saman, domin kuwa ko albashi bai kai ga fara amsa ba.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Manyan hakiman fadar Sarkin Kano guda 4 sun nuna ma Ganduje yatsa

An sallami wani ma’aikacin gwamnati saboda goyon bayan jam’iyyar APC a bayyane

Daniel
Source: UGC

Matashi Daniel mai shekaru 29, ya bayyana cewa a ranar 9 ga watan Mayu aka bashi takardar sallama daga aiki, takardar dake dauke da sa hannun shugaban sashin kula da daukan ma’aikata na kamfanin, Mista Idorenyin Eddie.

“Muna sanar da kai bamu bukatar aikinka, daga yanzu.” Inji wasikar, sai dai wasikar ta kara da cewa kamfanin zata biyashi albashin wata guda daya, da kuma iyaka kudin kwanakin da yayi yana aiki.

Sai dai Daniel ya shaida ma majiyarmu cewa a kwanakin baya wani abokin aikinsa ya shaida masa yadda wani babban jami’I a kamfanin, yayi korafi akansa na cewa yana sukar gwamnan jahar Akwa Ibom, Udom Emmanuel a shafinsa na Facebook.

Ya kara da cewa yafi zargin wani hadimin gwamnan, Aniekeme Finbarr da ruruta wannan magana tun bayan wani rubutu da yayi a shima a shafinsa na Facebook yana zargin cewa shi dan APC ne, kuma wai yana zagin Gwamna Udom.

Game da nuna bambanci ga ma’aikaci kuwa, sashi na 42 na kundin dokokin Najeriya ta haramta nuna wariya ga ma’aikaci akan ra’ayin siyasarsa, kabila, jinsi ko kuma addininsa, amma kwamishinan sufurin jirgin sama na jahar, Akan Okon yace bashi da masaniya game da sallamar Daniel.

Daga karshe Daniel yayi magiya ga Gwamna Udom daya mayar dashi bakinsa, sakamakon sai da ya kwashe shekaru shida a gida babu aikin yi, domin kuwa a cewarsa bashi da wata jahar data wuce jahar Akwa Ibom.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel