Akwai yiwuwar za'a kara farashin man fetur a Najeriya - Rewane

Akwai yiwuwar za'a kara farashin man fetur a Najeriya - Rewane

-Har yanzu bamu tsallake matakin karuwar farashin man fetur ba, inji wani kwararre akan harkokin shige da ficen kudi

-Akwai yiwuwar za'a kara farashin man fetur a Najeriya, inji Rewane

Wani masani kuma kwararre akan harkokin shige da fice kudi, Mista Bismarck Rewane yace tallafin man fetur da gwamnati ke biya ba karamin ci mata tuwo a kwarya yake ba.

Rewane yayi wannan furuci a wurin wani taro da aka gudanar a makarantar koyon kasuwanci ta Legas inda ya gabatar da wata takarda a ranar 8 ga watan Mayu.

Kada yan Najeriya su cire tsammani akan karuwar farashi man fetur, inji Rewane

Mista Bismarck Rewane
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Bankwana da mulki: Saraki ya bukaci hadimansa su rubuta takardar ajiye aiki

Kadan daga cikin abinda wannan takarda tasa ta kunsa shine, “ Bankin duniya yayi kiyasin kudin da gwamnatin Najeriya ta kashe domin biyan tallafin man fetur akan N731bn a shekarar 2018. A hankali ake kokari rage wannan kudi saboda a kasafin kudin shekarar 2019 an ware N305bn ne kacal domin biya tallafin.

Datse kashi 40 cikin dari na tallafin na nuna cewa akwai yiwuwar karuwar farashin man fetur.” Inji Rewane.

Kwararren akan harkokin kudi ya sake cewa, karuwar farashin man zai haifar da matsananciyar matsala saboda farashin saura ababe ma zai karu.

A cewarsa, Najeriya nada karancin samun haraji wanda shine yasa GDP dinmu yake kashi 5.3 cikin dari.

Inda ya bayyana kasafin kudin 2019 a matsayin abinda yakamata ace ya fito da Najeriya daga cikin matsalar da muke fama da ita ta tattalin arziki amma ba ya sake jefamu cikinta ba.

“ Kudaden shiga da ake samu ta hanyar man fetur, an hakaito raguwarsu saboda doka da kuma karfin hukumar OPEC akan abinda Najeriya zata iya fita dashi wata kasa.” Ya sake fadi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel