Ban ji dadin mugun zaman da muka yi da Saraki da Dogara ba – Inji Buhari

Ban ji dadin mugun zaman da muka yi da Saraki da Dogara ba – Inji Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yayi duba I zuwa ga irin rashin jituwa da aka yi ta samu tsakanin bangaren zartarwa da majalisar dokokin Najeriya, inda ya karkare cewa anyi mugun zama da juna, kuma bai ji dadin hakan ba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Buhari ya bayyana haka ne yayin da ya gayyaci shuwagabannin majalisar, Sanata Bukola Saraki da Kaakakin majalisa Yakubu Dogara zuwa fadar gwamnati domin zaman buda baki tare dashi a daren Talata, inda yace zaman da suka yi da juna bai kamata ba.

KU KARANTA: Shugaban EFCC ya bayyana babban dalilin da yasa suka kaddamar da bincike akan Saraki

Ban ji dadin mugun zaman da muka yi da Saraki da Dogara ba – Inji Buhari

Yayin shan ruwan
Source: Twitter

“Dangantaka tsakanin bangaren zartarwa da bangaren majalisa ba wani abin a yaba bane, amma ina fata dukkaninmu zamu yi iya bakin kokarinmu wajen ganin mun tabbatar da kyakkyawar dangantaka tsakanin bangaren zartarwa da majalisa ta 9 mai zuwa domin mu yi ma jama’a aiki yadda ya kamata.

“Ina kira ga masu girma Sanatoci da yan majalisa masu karamci dasu jajirce wajen binne duk wata bukatar kashin kai don ganin mun hada karfi da karfe don yi ma yan Najeriya aikin daya kamata, kuma kofata a bude take ga duk wani dan majalisa dake da wata shawara da zata inganta aikin gwamnati.” Inji shi.

A nasa bangaren, shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki ya bayyana ma shugaban kasa cewa a shirye majalisa take a kowanne lokaci wajen yi ma kasa hidima, don haka yace basu da wata matsala daga bangarensu.

Daga cikin wadanda suka halarci shan ruwan akwai kaakakin majalisa Yakubu Dogara, mataimakin shugaban majalisa, Ike Ekweremadu, mataimakin Kaakaki, Yusuf Lasun, shugaban masu rinjaye, Ahmad Lawan, shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, shuwagabannin masara rinjaye da mataimakansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel