Yaki da rashawa: Har yanzu mu na da tafiya mai nisan gaske - Osinbajo

Yaki da rashawa: Har yanzu mu na da tafiya mai nisan gaske - Osinbajo

A ranar Talatar da ta gabata mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya sake zayyana wata gazawa ta gwamnatin su karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Mataimakin shugaban kasar Najeriya a ranar Talatar da gabata ya bayyana cewa har ila yau akwai sauran rina a kaba wajen cimma nasara a fagen yaki da rashawa da ya kasance mafificin jigo na akidun gwamnatin su.

Yaki da rashawa: Har yanzu mu na da tafiya mai nisan gaske - Osinbajo

Yaki da rashawa: Har yanzu mu na da tafiya mai nisan gaske - Osinbajo
Source: Depositphotos

Furucin mataimakin shugaban kasar na zuwa ne yayin taron yaki da rashawa da kwamitin bayar da shawara ga shugaban kasa akan harkokin da suka shafi rashawa ya dauki nauyin gudanarwa cikin babban birnin kasar nan na tarayya.

Duk da cewa hakar su ba ta cimma ruwa ba cin galaba akan wannan mummunar annoba, cikin kyautata zato da tsammani mataimakin shugaban kasar ya ce akwai nasarori da dama da gwamnatin ta samu tun yayin da ta daura damarar yaki da rashawa a shekarar 2015.

KARANTA KUMA: Gwamnonin Kebbi da Zamfara sun ziyarci shugaba Buhari a fadar Villa

Cikin kalamansa Farfesa Osinbajo ya ce akwai sauran tafiya mai nisan gaske wajen cin galaba akan rashawa yayin da gwamnatin su ke kan gaba wajen gano hanyoyin warware sarkakiyar da kasar nan ke ciki. Ya buga misali da assassa asusun gwamnatin na bai daya.

A wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, mataimakin shugaban cikin nuna rashin jin dadin sa ya bayyana yadda kawowa yanzu akwai babban kaso na wasu yankuna da babu damar shiga a jihar Bornon sakamakon ta'addanci kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel