Rundunar soji ta fitar da jawabi a kan zargin yunkurin kifar da gwamnatin Buhari

Rundunar soji ta fitar da jawabi a kan zargin yunkurin kifar da gwamnatin Buhari

A yau, Talata 14 ga watan Mayu ne hedkwatan tsaro na kasa, DHQ ta nesanta kanta daga wata takarda da aka gano dauke da rubutu da ke kira a hambare gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Navy Capt. Muhammadu Wabi, mataimakin Direktan yadda labarai na DHQ ya yi ikirarin cewa wata kungiya mai suna "Nigerian Continuity and Progress (NCP)" ce ta wallafa takardan.

Wabi ya yi ikirarin takardan ta bukaci a kafa gwamnatin rikon kwarya a maimakon gwamnatin shugaba Buhari.

Rundunar soji ta fitar da jawabi a kan zargin yunkurin kifar da gwamnatin Buhari

Rundunar soji ta fitar da jawabi a kan zargin yunkurin kifar da gwamnatin Buhari
Source: UGC

DUBA WANNAN: Ba na son a kai maka farmaki, Buhari ya gargadi Osinbajo

"Dakarun Sojojin Najeriya (AFN) sun nesanta kansu daga tsageranci da ke dauke cikin wata takarda da wata kungiyar mara fuska mai suna Nigerian Continuity and Progress (NCP) ke yadawa na kira ga hambarar da gwamnatin demokradiyya mai ci yanzu da kuma kafa gwamnatin rikon kwarya.

"AFN tayi Allah wadai da wannan yunkuri da ya ci karo da demokradiyya da kuma yi tir da marubucin wannan takardan.

"Kazalika, ana kira ga jama'a suyi watsi da abinda wannan takardan ke dauke da shi na kira ga rushe demokradiyar da muka sha wahalar kafawa," inji sanarwan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Online view pixel