Bankwana da mulki: Saraki ya bukaci hadimansa su rubuta takardar ajiye aiki

Bankwana da mulki: Saraki ya bukaci hadimansa su rubuta takardar ajiye aiki

-Bukola Saraki ya fara bankwana da majalisar dattawa yayinda ya bukaci dukkanin hadimansa da su rubuto takardar ajiye aiki

-Wata wasika da fito daga ofishin shugaban ma'aikatan ofishin Saraki ce tayi bayani akan abinda yakamata takardar ta kunsa

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya fara shirya hannunta ragamar majalisar zuwa ga wanda zai kasance sabon shugaban majalisar dattawa ta 9 wanda lamarin da zai auku a makon farko na watan Yuni.

Bincike ya nuna cewa Saraki ya riga da ya kammala shirye-shiryensa inda ya umarci hadiminsa da su bashi takardun mika aiki.

Bankwana da mulki: Saraki ya bukaci hadimansa su rubuta takardar ajiye aiki

Bankwana da mulki: Saraki ya bukaci hadimansa su rubuta takardar ajiye aiki
Source: UGC

KU KARANTA:Agogo sarkin aiki: Gwamnan Legas mai barin gado Ambode

Har ila yau, Saraki ya shirya tsaf domin mika ragamar jagorancin majalisar zuwa ga wanda zai gajeta daga wajensa ba tareda da wata tangarda ba a watan gobe.

Haka zalika, zaman majalisa na karshe wanda Saraki zai jagoranta zai kama ne a makon farko na watan Yuni inda kuma bikin kaddamar da sabbin yan majalisa ta 9 zai biyo baya a ranar 11 ga watan Yuni.

“A cikin takardar da ta fito daga ofidhin Hakeem Baba Ahmed, shugaban ma’aikatan ofishin Saraki, an bukaci dukkan ma’aikatan su rubuta takardar barin aiki.

Ana so takardar ta kunshi cikakken sunan ma’aikaci, mukamin sad a irin nasarorin da ya samu yayin aiki da kuma duk wani bayani da yake ganin ya dace ya samu gurbi a cikin wasikar.” A cewar Hakeem Baba Ahmed.

Sai dai kuma, har ila yau Saraki bai bayyana wanda yake goyon baya ba cikin yan takarar shugabancin majalisar su uku; sanata Ahmad Lawan, sanata Muhammad Ali Ndume da kuma Muhammad Danjuma Goje.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel