Yanzu Yanzu: Buhari ya kafa kwamitin kaddamar da mafi karancin albashi

Yanzu Yanzu: Buhari ya kafa kwamitin kaddamar da mafi karancin albashi

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa kwamitin kaddamar da mafi karancin albashi

- An nada shugabar ma’aikata Winifred Oyo-Ita a matsayin shugabar kwamitin

- Gwamnatin tarayya ta ba kwamitin makonni hudu su cika aiki

Gwamnatin tarayya a ranar Talata, 14 ga watan Mayu ta kafa kwanitin kaddamar da sabon mafi karancin albashi, inda shugabar ma’aikata Winifred Oyo-Ita, ta kasance jagora.

Yayin kaddamar da kwamitin, babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, wanda ya kasance a madadin shugaba a kwanitin, yace kwamitin na da tsawon makonni hudu don kammala aikinta, inda zata fara zaman ta na farko a ranar 20 ga watan Mayu.

Daga cikin mambobin kwamitin akwai ministan kwadago da dibar ma’aikata, ministan kudi, ministan lafiya, ministan kasafi da tsare-tsare na kasa, da kuma ministan ilimi.

Yanzu Yanzu: Buhari ya kafa kwamitin kaddamar da mafi karancin albashi
Yanzu Yanzu: Buhari ya kafa kwamitin kaddamar da mafi karancin albashi
Asali: Facebook

Sauran sun hada da ministan shari’ah, Daraktan Janar na ofishin kasafi, sakataren hukumar shari’ah na tarayya, sakataren hukumar majalisar dokoki da shugaban hukumar albashi, kudaden shiga, wadanda zasu yi aiki a matsayin sakataren kwamitin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta soke fifikon da ke tsakanin HND da digiri a hukumomi 4

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi fashin baki da cewar kawowa yanzu akwai babban kaso na wasu yankuna da ma'aikatan lafiya ba su da damar samun shiga a jihar Borno sakamakon ta'azzarar ta'addancin kungiyar masu tayar da baya ta Boko Haram.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito a shafin ta na ranar Talata, 14 ga watan Mayun 2019, mataimakin shugaban kasa ya ce akwai al'umma da dama na jihar Borno da suka wanke kafafun su wajen tserewa zuwa wasu kasashe dake makotaka da Najeriya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel