Gwamnonin Kebbi da Zamfara sun ziyarci shugaba Buhari a fadar Villa

Gwamnonin Kebbi da Zamfara sun ziyarci shugaba Buhari a fadar Villa

A ranar Talata cikin fadar VIlla da ke babban birnin kasar nan na tarayya, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi ganawar sirri da gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu da kuma takwaran sa na jihar Zamfara, Abdulaziz Abubakar Yari.

Gwamnonin Kebbi da Zamfara sun ziyarci shugaba Buhari a fadar Villa

Gwamnonin Kebbi da Zamfara sun ziyarci shugaba Buhari a fadar Villa
Source: UGC

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, gwamnonin biyu sun isa fadar shugaban kasa a tare da juna inda suka kebance wajen ganawa da shugaba Buhari.

Kawowa yanzu babu masaniyar dalilin ziyarar su tare da abin da ganawar su ta kunsa a yayin da gwamnonin biyu suka yiwa manema labarai ta kurame bayan ganawar su da shugaban kasar a garin Abuja.

KARANTA KUMA: Mu ne ke da alhakin kashe sojojin Najeriya 11 - ISIS

Shugaban kasa Buhari a ranar Litinin ya gudanar da makamanciyar wannan ganawa da gwamnan jihar Legas Akinwunmi Ambode, gwamnan jihar Anambra Cif Willie Obiano, Mallam Nasir El-Rufa'i, gwamnan jihar Kaduna da kuma gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel