Shugabancin majalisa: Gbajamiamila ya zabi abokin takara

Shugabancin majalisa: Gbajamiamila ya zabi abokin takara

Daya daga cikin manyan masu neman takarar kujerar kakakin majalisar wakilai na tarayya a majalisa karo na 9, Femi Gbajabiamila ya zabi Hon. Ahmed Wase daga jihar Plateau a matsayin abokin takararsa.

Kungiyar yakin neman zaben Gbajabiamila ne ta sanar da hakan a harabar majalisar tarayya a ranar Talata.

Direkta Janar na kungiyar yakin neman zaben Femi Gbajabiamila, Abdulmumeen Jibril ya ce bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki kungiyar ta cimma matsayar zaben Honorable Ahmed Wase a matsayin abokin takarar Gbajabiamila.

Shugabancin majalisar wakilai na tarayya: Gbajamiamila ya zabi abokin takara

Shugabancin majalisar wakilai na tarayya: Gbajamiamila ya zabi abokin takara
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Dan takarar shugaban kasa ya saka baki cikin kirkirar sabbin masarautun Kano

Abdulmumeen ya ce zabin Wase alheri ga 'yan Najeriya.

A cewar Jibril, "Muna son mu sanar da ku cewa muna da adadin mambobin da za su jefa mana kuri'a mu lashe zabe a ranar 10 ga watan Yuni.

"Cikin makonni shida da suka gabata, munyi amfani da hanyoyi daban-daban har da kimiyya domin jinjina yuwawar samun nasarar mu. Mun gamsu cewa yanzu muna da adadin kuri'u da za mu iya lashe zabe."

Jibril ya yi bayanin cewa sun bulo da wata hanya inda mambobin mu suka tabbatar mana dan takarar da za su zaba a rubucce.

Ya kara da cewa 'yan jam'iyyar adawa ta PDP da wasu jam'iyyun za su zabe dan takararsu.

Ya ce Gbajabiamila/Wase da wasu za suyi tafiya tare da kowa ba tare da nuna banbancin jam'iyya ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel