Shugaban EFCC ya bayyana babban dalilin da yasa suka kaddamar da bincike akan Saraki

Shugaban EFCC ya bayyana babban dalilin da yasa suka kaddamar da bincike akan Saraki

Shugaban hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, Ibrahim Magu ya bayyana cewa babu wata gaba ko rashin jituwa a tsakaninsa da shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki a binciken da suka kaddamar akansa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Maga yana cewa duk wanda kaga hukumar EFCC ta gayyata toh tana zarginsa ne da aikata laifukan da suka shafi rashawa da cin hanci, kamar yadda ya fada a ranar Talata 14 ga watan Mayu a ofishin hukumar dake Abuja.

KU KARANTA: Babbar mota makare da fasinja ta kama ci da wuta a jahar Legas, ta kone kurmus

Shugaban EFCC ya bayyana babban dalilin da yasa suka kaddamar da bincike akan Saraki
Magu da Saraki
Source: UGC

Magu ya bayyana haka ne yayin da yake amsa tambayar da wani yayi masa akan menene dalilin da yasa EFCC ke bankado tsofaffin laifuka tana bincikensu, sai ya kada baki yace “A’a ba wai muna masa bita da kulli bane, kamar yadda muke bincikar kowa haka shima muke bincikarsa.

“”EFCC bata farautar wanda bashi da laifi, idan kai ba barawo bane ba zamu fara farautarka haka nan ba, idan mutum ba dan damfara bane ba zamu kwankwasa masa gida ba, sai mun yi bincike na karkashin kasa sosai har tsawon watanni shida kafin mu fara neman mutum, a wasu lokutan ma sai mu kwashe shekaru biyar muna bincike.

“Rashawa babbar matsala ce ga Najeriya, kuma ya kamata kowa ya hada hannu wajen yakarta, idan har muka yaki cin hanci da rashawa a Najeriya, toh mun yaki bala’o’i kamarsu Boko Haram, hare haren yan bindiga da sauransu, duk rashawace kanwa uwar gami.”

Wannan sabuwar tataburza tsakanin EFCC da Saraki ta faro ne tun makon daya gabata bayan wata takarda da EFCC ta aika ma Saraki inda take neman karin bayani game da albashinsa da alawus alawus dinsa a zamanin da yake gwamnan jahar Kwara.

Sai dai Sarakin ya bayyana wannan bukata ta EFCC a matsayin cin fuska, amma hukumar ta bayyana masa cewa ya kwantar da hankalinsa idan har bashi da guntun kashi a gindinsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel