Sojoji sun kashe masu zanga-zangar lumana 6 a Sudan

Sojoji sun kashe masu zanga-zangar lumana 6 a Sudan

A kalla masu zanga-zangar neman mulkin dimokradiyya 6 ne aka kashe, aka kuma raunata wasu da dama yayin zaman dirshan din da suke yi, kamar yadda wani likitan gwamnatin kasar Sudan ya tabbatar a ranar Talata.

Sai dai, a daren ranar Litinin, gwamnatin rikon kwarya ta soji a kasar ta musanta far wa masu zanga-zangar da suka hedikwatar a Khartoum, babban birnin Sudan.

Tun farkon shigowar shekarar nan 'yan kasar ta Sudan suka fara zaman dirshan a wani salon zanga-zangar nuna adawa da gwamnati, lamarin da ya yi sanadiyar saukar shugaban kasar na tsawon shekaru, Omar al-Bashir.

A cikin wani jawabi da ta fitar, gwamnatin kasar ta zargi wasu bata gari da shiga cikin masu zanga-zangar tare da kawo hargitsi ta hanyar yin harbin bindiga da kuma kai wa jami'an tsaro farmakai.

"Wasu batagari ne suka shiga cikin masu zanga-zangar dake zaman dirshan domin kawo hargitsi, sun harba bindiga tare da kai farmaki domin haddasa fitina tsakanin dakarun soji da masu zanga-zanga na gaskiya," a cewar jawabin.

Sojoji sun kashe masu zanga-zangar lumana 6 a Sudan
Zanga-zanga a Sudan
Source: Twitter

Jawabin ya kara da cewa daga cikin wadanda suka mutu akwai sojoji uku, yayin da wasu sojojin uku suka samu raunuka.

DUBA WANNAN: Rundunar Abba Kyari ta samu gagarumar nasara a kan masu garkuwa da mutane a hanyar Abuja (Hotuna)

Harin da aka kai kan fararen hular na zuwa bayan masu zanga-zangar sun kara mamaye titunan garin Khartoum a ranar Litinin domin tilasta gwamnatin rikon kwarya ta soji ta mika mulki ga farar hula bisa zarginsu da cewar yaran tsohon shugaban kasa al-Bashir ne.

Da farko, jami'an 'yan sanda da dakarun soji sun yi kokarin tarwatsa daruruwan masu zanga-zangar ta hanyar amfani da barkonon tsohuwa da kulki amma hakan ya ci tura.

Gwamnatin sojin da kungiyoyin hamayya sun fitar da wata sanarwa ranar Litinin dake cewa sun cimma matsayar kafa gwamnatin hadin gwuiwa tun karshen watan Afrilu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel