Bola Tinubu: Ina nan a kan matsayata har gobe inji Gwamna El-Rufai

Bola Tinubu: Ina nan a kan matsayata har gobe inji Gwamna El-Rufai

Mai girma gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya fito ya sake bayyana cewa ba ya bukatar ya nemi afuwa a kan kalaman da yayi a game da yadda za a daina siyasar Uban-gida a Najeriya.

Gwamnan yayi wannan jawabi ne kwanaki a Legas inda ya bayyana yadda za a bi wajen kawo karshen wasu ‘yan siyasa da ake ganin sun fi karfin kowa a kasar. Wannan kalamai na gwamnan sun jawo masu surutu musamman a Legas.

Sai dai duk da ce-ce-ce-ken, wannan bai dagawa gwamnan hankali ba, inda yace ya fadi irin na sa ra’ayin ne kuma sai dai ayi duk abin da za ayi, amma gwamnan da yake magana a makon nan, yace bai zai nemi afuwar kowa ba.

KU KARANTA: Nasir El-Rufai bai nufi ci wa Bola Tinubu mutunci ba – inji APC

Bola Tinubu: Ina nan a kan matsayata har gobe inji Gwamna El-Rufai

Ana alakanta wasu kalaman Gwamnan Kaduna da Jigon APC Bola Tinubu
Source: Twitter

Gwamna El-Rufai yayi wannan jawabi ne a Ranar Litiin 13 ga Watan Mayu a fadar shugaban kasa, bayan ya gana da Muhammadu Buhari. Gwamnan yace don kurum kalamansa ba su yi wa wasu dadi ba, ba zai fito yana mai bada hakuri ba.

Nasir El-Rufai ya kai ziyara zuwa fadar ta Aso Villa ne domin yi wa shugaban kasa Buhari bayanin halin tsaro a hanyar jihar Kaduna zuwa Abuja. El-Rufai tare da wasu gwamnonin kasar ne su ka sa labule da shugaban kasar a fadarsa jiya.

Da ake sake bijirowa gwamnan da tambaya a kan maganganun da yayi kwanaki a Legas, sai yace yana da damar furta ra’ayin siyasarsa a matsayinsa na ‘dan kasa. El-Rufai yace mulkin farar hula ake yi a wanda ya ba kowa ‘yanci magana.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel