Hazikin dalibin jami'ar Nsukka ya kashe kan sa

Hazikin dalibin jami'ar Nsukka ya kashe kan sa

Chukwuemeka Akachi, wani hazikin dalibin jami'an Najeriya da ke Nsukka, UNN, ya kashe kansa bayan ya dade yana fama da matsalar kwakwalwa.

Mr Akachi, wadda ke karatu a tsangayar nazarin harshen turanci ya kashe kansa ne a ranar Lahadi 12 ga watan Mayu.

A cikin wasu rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Akachi ya bayyana yadda ya dade yana fama da ciwon kwakwalwa da kuma yadda ciwon ke kawo masa cikas a rayuwa.

Hazikin dalibin jami'ar Nsukka ya kashe kan sa
Hazikin dalibin jami'ar Nsukka ya kashe kan sa
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Dan takarar shugaban kasa ya saka baki cikin kirkirar sabbin masarautun Kano

Mr Akachi ya kara da cewa ya dade yana rai hannun Allah ana masa magani a asibiti

A cewarsa, irin rayuwarsa na da matukar tsada.

"Ina mika godiya ta ga 'yan uwa da abokan arziki na da suke bani kwarin gwiwa yayin a yayin da na ke fama da wahalwalu.

"Ina mika godiya ta ga wadanda suka kira ni da wanda suka aiko min sakon tes. Ina fata ba za mu taba manta juna ba.

"Akwai yiwuwar kun kara min sa'o'i, kwanaki ko watanni cikin rayuwata amma kun san maganin da ake min yana da matukar tsada," kamar yadda Mr Akachi ya rubuta a shafinsa na Facebook sa'o'i kafin rasuwarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Online view pixel