Gwamnan Yobe Dankwambo ya nemi a saki Leah Sharibu yayinda ta cika shekara 16

Gwamnan Yobe Dankwambo ya nemi a saki Leah Sharibu yayinda ta cika shekara 16

Gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Hassan Dankwambo, a ranar Talata, 14 ga watan Mayu ya bukaci ayi gaggawan sakin Leah Sharibu, wacce ta rage a hannun yan Boko Haram tsawon watanni da dama.

Dankwambo ya kuma tura sakon zagayowar ranar haihuwa ga yarinyar wacce ke tsare a hannun Boko Haram, bayan sun sac eta tare da sauran daliban makarantar Dapchi, a ranar 19 ga watan Fabrairu, 2018.

Har yanzu tana hannn yan ta’addan bayan taki amsa addinin Musulunci yayinda aka saki sauran yarn da aka ace tare da ita.

“Barka da cika shekaru 16 ga Leah Sharibu. Ba za a taba mantawa da ke ba! Kina a zuciyarmu da addu’o’inmu. Allah karo shekaru masu yawa,” Dankwambo ya wallafa a shafinsa na zumunta inda anan ya kuma nemi a sake ta.

KU KARANTA KUMA: Wata kungiya ta maka hukumar yan sanda da EFCC a kotu, tace lallai sai an binciki Ganduje

A baya Legit.ng ta rahoto cewa wata budurwa, wacce ta sha da kyar daga hannun 'yan Boko Haram, ta bayyanawa wasu 'yan jarida, yanda haduwar ta da Leah Sharibu ta kasance a sansanin 'yan Boko Haram, dake cikin dajin Sambisa. Sannan matar ta bayyana yanda wasu mata da jarirai guda takwas suka rasa rayukan su, a lokacin da suke kokarin guduwa daga sansanin 'yan Boko Haram din.

Budurwar mai shekaru 25 ta bayyana sunan ta da Ruth, tace tun lokacin da 'yan ta'addar suka kama ta, shekaru biyar da suka wuce, tace sun tilasta ta akan ta bar addinin ta na Kiristanci ta koma addinin Musulunci.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel