Yanzu yanzu: Buhari zai tafi Saudiya sau biyu cikin makonni biyu

Yanzu yanzu: Buhari zai tafi Saudiya sau biyu cikin makonni biyu

Shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyara kasar Saudiya sau biyu kafin karshen wannan watan.

Wannan ziyarar na zuwa ne bayan ziyarar da shugaban kasar ya kai birnin Landan inda ya tafi a ranar 24 ga watan Afrilu ya kuma dawo a ranar 5 ga watan Mayu kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

Shugaban kasan zai tafi Makkah da Madina ne domin yin umara daga ranar 15 ga watan Mayu zuwa ranar 22 ga watan Mayun 2019.

Yanzu yanzu: Buhari zai tafi Saudiya sau biyu cikin makonni biyu

Yanzu yanzu: Buhari zai tafi Saudiya sau biyu cikin makonni biyu
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Dan takarar shugaban kasa ya saka baki cikin kirkirar sabbin masarautun Kano

Bayan shugaban kasar ya dawo Najeriya, zai kuma sake komawa kasar Saudiya domin hallartar Organisation of Islamic Organisation (OIC) a Jeddah daga ranar 30 ga watan Mayu zuwa ranar 1 ga watan Yunin 2019.

Zai yi tafiyar karo na biyu ne sa'o'i kadan bayan an rantsar da shi karo na biyu kan mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2019.

Hallartan taron na OIC zai janyo cece kuce duba da cewa wasu sun dade suna zargin cewa shugaban kasar yana nuna fifiko ga wata addini a kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel