Wani matashi ya aika da kaninshi lahira

Wani matashi ya aika da kaninshi lahira

- Wani saurayi ya shiga hannun hukuma, inda ta yanke mishi hukuncin kisa bayan ta kamashi da laifin kashe kaninsa

- Saurayin ya yi amfani da kwalba inda ya dinga cakawa kanin nasa har sai da ya ga ya bar duniya

Babbar kotun jihar Legas ta yankewa wani matashi dan shekara 33, mai suna Allen Abiodun hukuncin kisa, bayan ta kama shi da laifin kashe kaninsa mai suna Wale.

Kotun wacce alkalin kotun Raliatu Adebiyi ta ke shugabanta, ta tabbatar faruwar lamarin.

A lokacin da alkalin ta ke bayyana hukuncin mai laifin, ta bayyana cewa wanda ake tuhumar wanda ya ke dan shekaru 27 a duniya a lokacin da lamarin ya faru, ya bayyana cewa an tashe shi daga bacci ne, inda ya ga kaninshi, Wale Allen, a tsaye a kanshi da kwalba a hannu.

Wani matashi ya aika da kaninshi lahira
Wani matashi ya aika da kaninshi lahira
Source: Depositphotos

Wanda ake tuhumar ya bayyana cewa cikin gaggawa ya rike kwalbar ya cikawa dan uwannashi, wanda ya mutu a take a wurin. Domin ganin ya rufa ma kanshi asiri sai ya ja gawar marigayin ya kai ta cikin daji ya rufe ta da ganye.

Alkalin ta kuma bayyana cewa wanda ake tuhumar ya bayyana cewa kanin nashi ya sha fada masa cewa sai ya kashe shi, inda shi kuma ya ke mayar masa da amsa cewa sai ya mutu kafin shi.

KU KARANTA: Gaskiyar labarin da ke nuna cewa Yusuf Buhari ya mallaki dala biliyan 2.3

A lokacin shari'ar wanda ake tuhumar ya nesanta dangantakarshi da mahaifiyar shi da kuma marigayin, inda ya bayyana cewa mahaifiyarsa 'yar kasar China ce.

Duk da bayanin da ya yi, alkalin ta bayyana cewa shaidu sun nuna cewa ya yi kisan kai.

Yayin da ta ke gabatar da hukuncin akan mai laifin, ta bayyana cewa kotu ta yanke mishi hukuncin kisa, bisa kama shi da laifin kashe kaninsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit

Online view pixel