Wata kungiya ta maka hukumar yan sanda da EFCC a kotu, tace lallai sai an binciki Ganduje

Wata kungiya ta maka hukumar yan sanda da EFCC a kotu, tace lallai sai an binciki Ganduje

Wata kungiyar jama’a mai suna Enough is Enough (EiE) Nigeria, tam aka hukumar yaki da cin hanci da rashawa a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja akan zargin cin hanci da ake yiwa Abdullahi Ganduje, gwamnan jihar Kano.

Kungiyar ta ambaci sunayen hukumar yaki da rashawa ta ICPC da rundunar yan sanda a cikin wadanda ake kara a cikin takardar karar.

A watan Oktobar shekarar da ta gabata ne jaridar Daily Nigerian ta wallafa wasu bidiyo daban-daban da ke nuna Ganduje yana karban rashawa daga hannun yan kwangila, amma gwamnan ya karyata zargin.

Hakazalika majalisar dokokin Kano ta kafa kwamitin mutum bakwai domin bincike akan lamarin gwamnan, sai dai babbar kotun jihar ta dakatar da majalisa daga binciken.

Wata kungiya ta maka hukumar yan sanda da EFCC a kotu, tace lallai sai an binciki Ganduje

Wata kungiya ta maka hukumar yan sanda da EFCC a kotu, tace lallai sai an binciki Ganduje
Source: Depositphotos

Amma kungiyar ta EiE caccaki martanin hukumomin akan lamarin.

A wani jawabi da ta saki a ranar Talata, 14 a watan Mayu, Tolulope Oladele, matimakiyar manajan kungiyar, tace kungiyar ta jajirce domin neman jawabi daga zababbun jami’an gwamnati a kasar.

KU KARANTA KUMA: Ba na son a kai maka farmaki, Buhari ya gargadi Osinbajo

A gefe guda, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Musa Kwankwaso, hakimin karamar hukumar Madobi kuma mahifi ga tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya janye biyayyar sa ga sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

A cikin satin da ya gabata ne gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya rattaba hannu a kan dokar masarauta da majalisar dokokin jihar tayi wa garambawul.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel