Ashiru ya nemi a sake kidiya kuri'un zaben gwamna na jihar Kaduna

Ashiru ya nemi a sake kidiya kuri'un zaben gwamna na jihar Kaduna

Dan takarar gwamna karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP a zaben 2019 a jihar Kaduna, Isha Ashiru ya shigar da izinin neman kotu ta bayar da umurnin sake kidaya kuri'un.

Jastis Boko ya dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 25 ga watan Mayu domin bawa Hukumar INEC da sauran bangarori biyu da ake shari'ar dasu su mayar da martani a kan bukatar na PDP.

"Mun shigar da takardan neman a sake kidaya kuri'un da aka kada yayin zaben.

"Hakan na da muhimmanci ko zai zama hujja na nuna cewa mafi yawancin sakamakon zaben da aka sanar ba hakan su ke ba.

Ashiru ya nemi a sake kidiya kuri'un zaben gwamna na jihar Kaduna

Ashiru ya nemi a sake kidiya kuri'un zaben gwamna na jihar Kaduna
Source: UGC

DUBA WANNAN: Dan takarar shugaban kasa ya saka baki cikin kirkirar sabbin masarautun Kano

"Muna fatan sakamakon kidayan za su nuna cewa jam'iyyar PDP ce tayi nasara a zaben.

"Kawai an kirkiri sakamakon zabe na bogi ne domin a nuna cewa jam'iyyar APC ce ta lashe zaben," a cewar Kurah.

A bangarensa, Abdulhakeem Mustapha, lauyan gwamna Nasiru El-Rufai ya shaidawa manema labarai cewa jam'iyyar PDP da dan takarar ta Isha Ashiru sun shigar da kararraki guda hudu marasa kan gado.

"Zamu kare nasarar mu a kotun. Kotu ta bamu sabon ranar da zamu gabatar da hujojin mu.

"Mun fara shaidawa kotu cewa karar ba ta da inganci. PDP da Ashiru suna neman a kidaya kuri'u a kotu amma ba zamu amince da hakan ba."

"Zamu kare nasarar da jama'an Kaduna suka bawa gwamna. Za mu gamsar da kotu cewa karar ba ta inganci saboda haka ayi watsi da ita."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel