Kana iya neman izinin bincikar dan sanda kafin shi ya bincike ka – Frank Mba

Kana iya neman izinin bincikar dan sanda kafin shi ya bincike ka – Frank Mba

- Hukumar yan sanda ta sanar da cewa mutum na da yancin bincikar jami’an yan sanda a yanayi da idan jami’an na shirin gudanar da wani bincike

- Kakakin rundunar yace mutum na iya neman izinin binciken jami’in dan sanda saboda kore shakku

- Mba ya kuma bayyana cewa mutum na da yancin neman sanin dalilin kama shi a duk lokacin da ake shirin yin wani kamu.

Rundunar yan sandan Najeriya ta bayyana cewa yan Najeriya na da yancin bincikar jami’an yan sanda a yanayi da idan jami’an na shirin gudanar da wani bincike.

Kakakin rundunar yan sandan Najeriya, Frank Mba ne ya bayyana hakana wani jawabi da ya saki a ranar Litinin, 13 ga watan Mayu.

Kana iya neman iziin bincikar dan sanda kafin shi ya bincike ka – Frank Mba
Kana iya neman iziin bincikar dan sanda kafin shi ya bincike ka – Frank Mba
Source: UGC

Mba yace a kokarin kawar da tsoro ko shakku, mutum na iya neman izinin binciken jami’in dan sanda kafin ya bari a bincike shi.

A cewar jawabin Mba, mutane na da yancin neman sanin dalilin kama su a duk lokacin da ake shirin yin wani kamu.

KU KARANTA KUMA: Osinbajo ya yi magana a kan halayen Abba Kyari da Lai Mohammed a cikin ramadana

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa, tawagar DCP Abba Kyari ta IRT dake karakashin ofishin babban sifeton y'an sanda na kasa (IGP) sun yi nasarar kama wasu gungun barayi da garkuwa da mutane da suka fitini hanyar Abuja zuwa Kaduna.

An samu miyagun makamai da suka hada da bindiga kirar AK47 guda biyu (2), ma'ajiyar harsashin bindiga guda hudu (4), harsashin bingida guda hamsin da hudu (54), bindiga baushe (Dane gun) guda biyar (5), da kuma shanun sata guda dari biyu (200) a wurin masu garkuwa da mutanen.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Online view pixel