Ka bar sa baki cikin lamuran yaki da cin-hanci, wata kungiya tayi kira ga AGF

Ka bar sa baki cikin lamuran yaki da cin-hanci, wata kungiya tayi kira ga AGF

-Wata kungiya ta shawarci Alakalin alkalai da ya bar shiga cikin laifukan cin hanci

-Kungiyar mai suna HEDA tace a matsiyanshi na ministan shari'a na kasa ba halayyar da yakamata ace ya nunawa ba kenan

Kungiyar Human and Environmental Development Agenda (HEDA) tayi kira ga Alkalin alkalai na kasa Abubakar Malami da ya bar sanya baki cikin yaki da cin hanci wanda hukumomin da abin ya shafa keyi.

Kungiyar a wata takardar da shugabanta, Olanrewaju Suraju ya sanyawa hannu ta zargi Alkalin alkalan da kawo nakasu a wasu daga cikin laifukan cin hanci da rashawa ta hanyar shiga cikin lamarin da bai shafesa ba.

Ka bar sa baki cikin lamuran da suka shafi yaki da cin-hanci, wata kungiya tayi kira ga AGF

Ka bar sa baki cikin lamuran da suka shafi yaki da cin-hanci, wata kungiya tayi kira ga AGF
Source: Twitter

KU KARANTA:Yan bindiga sun kashe jami'an JTF 6 a Zamfara

“ A matsayinmu na kungiya, mun ga cewa ya dace mu fito muyi magana akan abinda AGF keyi na kokarin kawo cikas akan yaki da cin hanci wanda akeyi a halin yanzu a kasar nan.

HEDA ta bayyana a wurare da dama inda AGF ke cewa shifa baya goyon bayan daruruwan yan Najeriya akan yaki da cin hancin da akeyi a kasar nan.” Inji shugaban HEDA.

Kungiyar ta sake cewa, shi AGF a matsayinsa na ministan shari’a na kasa kamata yayi ya kasance jagoran wannan yaki, ba wai ya sanyawa jama’a shakku ba akan cewa yaki da cin hancin bai kunshi komi ba in banda siyasa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel