Al-Makura ya taka rawar gani a Nasarawa, inji Kakakin majalisa

Al-Makura ya taka rawar gani a Nasarawa, inji Kakakin majalisa

-Tanko Al-Makura ya sauya jihar Nasarawa fiye da lokacin da ya karbi jihar a 2011, inji Balarade Abdullahi

-Jihar Nasarawa ta samu cigaba kwarai da gaske a cewar Kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa

Kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa, Alhaji Ibrahim Balarabe Abdullahi yace Gwamna Tanko Al-Makura zai bar Nasarawa cikin kyakkyawan yanayi fiye da yadda ya karbeta a shekarar 2011, a ranar 29 ga watan Mayu da zai mika ragamar mulki zuwa ga sabon gwamnan jihar.

Balarabe Abdullahi yayi wannan furucin ne ranar Talata a Lafia babban birnin jihar yayinda yake zantawa da manema labarai.

Al-Makura yayi rawar gani a Nasarawa, inji Kakakin majalisa

Gov Tanko Al-Makura
Source: Twitter

KU KARANTA:Yan bindiga sun kashe jami'an JTF 6 a Zamfara

Yace gwamnatin Al-Makura ta habbaka tattalin arzikin jihar da kuma al’amuran jama’a na yau da kullum cikin wa’adin mulkinta.

“ Al-Makura ya karbi mulki jihar nan a shekarar 2011, lokaci bana cikin gwamnati amma dai ina bibiyar al’amuran gwamnatin tasa.

“ Idan baku manta ba, lokaci da Gwamna Al-Makura ya hau mulki anayiwa babban birnin jihar Nasarawa wato Lafia da kirari a matsayin wata kwaryakwaryar karamar hukuma wacce bata da komi.

“ Zuwan Al-Makura ya sauya jihar Nasarawa tamkar ba ita ba. Duk wanda yasan Nasarawa a shekarun baya yazo a yanzu tabbas zai ga canji.

“ 29 ga watan Mayu na dada gabatowa, hakika gwamna Al-Makura ya inganta jihar Nasarawa fiye da yadda ya karbe ta a shekarar 2011.” Inji kakakin majalisar.

Balarabe ya sake bayyana cewa, wannan cigaban da jiharsu ta samu ya kasance sanadiyar hadin kai tsakanin majalisar dokokin da kuma majalisar zartaswan jihar.

Ya kuma yi kira ga jama’ar jihar da su baiwa gwamnati mai shigowa goyon baya domin ciyar da jihar tasu gaba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel