Ramadan: An gano yan sandan Qatar na bai wa direbobi Musulmai kayan bude-baki

Ramadan: An gano yan sandan Qatar na bai wa direbobi Musulmai kayan bude-baki

Jami’an yan sanda a kasar Qatar sun yanke shawarar yin aikin lada ta hanyar yin sadaka a wannan wata mai falala na Ramadan. Sun aikata hakan ne ta hanyar rabama matafiya a hanya kayayyakin bude-baki.

Wadannan jami’ai na yan sanda a Qatar na tsayawa akan hanya don rabon kayan shan ruwa ga Musulmai da ke tafiya a hanya.

Suna haka ne domin matafiyan su bude-bakinsu a lokacin da ya kamata. An wallafa hotunan wadannan yan sanda da ke aikata hakan ne a shafin Twitter.

Wani shafin Twitter mai suna @RadicalYouthMan ne ya wallafa hotunan. Inda yake godiya ga wannan aiki na alkhairi da jami’an ke yi.

Kalli yadda ya rubuta a shafinsa a kasa:

“Wadannan jami’an yan sandan Qatar ne suna rabon kayan bude-baki ga mutanen da cunkoson ababen hawa ya cika dasu a hanya, domin su samu bude-bakinsu. Wadannan mutane ne kamar yan Najeriya. Jini ne ke yawo a jijiyoyinsu. Kalli, munemusababbin matsalolinmu. Ina kwana.”

KU KARANTA KUMA: Osinbajo ya yi magana a kan halayen Abba Kyari da Lai Mohammed a cikin ramadana

Tabbass, Ramadan lokaci ne da ya kamata Musulmai su dunga wanzar da aminci a tsakaninsu. Don haka, akwai wasu abubuwa da ya kamata a daina a wannan lokaci.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel