FG za ta kafa kwamitin kaddamar da sabon karin albashi

FG za ta kafa kwamitin kaddamar da sabon karin albashi

A ranar Talata ne gwamnatin tarayya ta sanar da cewar za ta kafa wani kwamiti da zai jagoranci kaddamar da sabon karin albashi, kusan wata guda bayan shugaba Buhari ya 'sa hannu' a kan dokar yin karin albashi.

Dakta Chris Ngige, ministan kwadago da samar da aiyuka, ne ya sanar da hakan yayin da yake amsa tambayoyi a gidan talabijin dangane da lokacin fara biyan sabon albashin.

Ngige bai bayyana lokacin da gwamnatin tarayya za ta fara biyan sabon albashin ba, sai dai ya ce za a biya ma'aikata ariyas duk lokacin da biyan sabon albashin ya fara.

Ya ce akwai matakai da siradai da sabon albashin zai bi kafin a fara biyan ma'aikata duk da cewar ya zama doka.

"Akwai matakai masu yawa da dole sai an bi su kafin fara biyan karin albashin, dole sai hukumar tsara biyan albashi ta kammala aikinta kafin a kaddamar da sabon karin," a cewar ministan.

FG za ta kafa kwamitin kaddamar da sabon karin albashi

Chris Ngige
Source: UGC

Ministan ya kara da cewa shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya, Winifred Oyo-Ita, ce zata shugabancin kwamitin da zai kunshi ministoci guda bakwai.

DUBA WANNAN: Zargin cin hanci: Ko majalisa zata tabbatar da gwamnan CBN?

Sannan ya kara da cewa dukkan ma'aikan Najeriya, na gwamnati da masu zaman kan su, za a ke biyan su N30,000 a matsayin mafi karancin albashi.

Ya ce ma'aikatan dake daukan ma fi karancin albashi da ya fi sabon albashin da aka kara, za a daidaita musu albashin da suke dauka.

Tuni shugaban kwadago ta kasa (NLC), Ayuba Wabba, ya bayyana damuwar sa a kan jan kafar da gwamnati ke yi wajen kaddamar da karin albashin bayan tabbatar da shi a matsayin doka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel