Osinbajo ya yi magana a kan halayen Abba Kyari da Lai Mohammed a cikin ramadana

Osinbajo ya yi magana a kan halayen Abba Kyari da Lai Mohammed a cikin ramadana

Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo yace ba zai iya tabbatar da cewa ko azumin Ramadana yayi tasiri akan halayen ministan labarai, Lai Mohammed, ministan ilimi, Adamu Adamu da kuma Shugaban ma’aikatan Buhari, Abba Kyari ba.

Osinbajo wanda yayi Magana a lokacin da Buhari ya gayyace shi da wasu ministoci shan ruwa a fadar Shugaban kasa a ranar Litinin, 13 ga watan Mayu, yace wasu dalilai sun sanya shi duba izuwa ga watan Ramadan amma sai ya tarar da akasin haka a lokacin da aka shiga watan.

A cewarsa, daya daga cikin dalilan shine cewa abokansa kan “guje ma matsala a lokacin Ramadan,” amma ba zai yi bayar da tabbacin haka ba akan Mohammed, Adamu da Kyari a wannan shekarar.

Osinbajo ya yi magana a kan halayen Abba Kyari da Lai Mohammed a cikin ramadana
Osinbajo ya yi magana a kan halayen Abba Kyari da Lai Mohammed a cikin ramadana
Source: UGC

Osinbajo yace wani kalubale kuma shine cewa Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa mafi tsawo a tarihi a wannan watan na Ramadana.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An nemi kotun zabe ta dakatar da rantsar da Buhari

Yace yana ta duba zuwa Ramadan saboda taron majalisa kan kasance a gajere a watan amma “kada mu kuma sanya ran cewa zaman majalisar na iya zama gajere a watan Ramadan."

Mataimakin Shugaban kasar ya bukaci mahalartan taron da suyi amfani da wannan lokaci da Ramadana wajen tunatar da kansu cewa hakkin da ya rataya ne a wuyansu kula da jin dadin yan Najeriya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Online view pixel