Majalisa ta fara shirin tabbatar da babban gwamnan CBN

Majalisa ta fara shirin tabbatar da babban gwamnan CBN

A ranar Talata ne majalisar dattijai ta fara daukan matakan tabbatar da Godwin Emefiele a matsayin babban gwamnan bankin kasa (CBN) a karo na biyu.

Shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, ya karbi wasikar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika ta neman tabbatar da sabunta nadin Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) a karo na biyu a cikin makon jiya.

Saraki ya karanta wasikar da shugaba Buhari ya aike a zauren majalisa ranar Alhamis.

Wasikar mai taken 'sabunta nadin Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya' ta isa ofishin shugaban majalisar dattijai a ranar 9 ga watan Mayu, 2019.

Majalisar ta mika wasikar ta shugaba Buhari zuwa kwamitin ta na harkokin banki da inshora domin daukan matakan da suka dace.

Majalisa ta fara shirin tabbatar da babban gwamnan CBN

Buhari da Emefiele
Source: Twitter

wannan na zuwa ne a daidai lokacin da majalisar ta karbi korafe-korafen zargin Emefiele da cin hanci.

Yanzu kallo ya koma kan majalisar domin ganin hanyar da za ta bi domin binciken zargin da ake yiwa Emefiele kamar tabbatar da shi.

DUBA WANNAN: Mayar da Emefiele: Kungiyar AFAN ta jinjina wa Buhari

A ranar Litinin ne gwamnan babban bankin kasa (CBN), Godwin Emefiele, ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar sa dake Abuja.

Cikin murmushi da annashuwa, Emefiele ya gaisa da shugaba Buhari a lokacin da shugaban kasa ke taya shi murna.

Wasu na ganin cewar ziyarar ta Emefiele ba za ta rasa nasaba da zargin da ake yi masa na yin sama da fadi da kimanin biliyan N500 ba, masu wannan hasashe na tunanin cewar Emefiele ya ziyarci Buhari ne domin ya wanke kan sa daga zargin badakalar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel