Ba na son a kai maka farmaki, Buhari ya gargadi Osinbajo

Ba na son a kai maka farmaki, Buhari ya gargadi Osinbajo

Shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo a kan shirin Market Moni daya daga cikin shirye shiryen rage radadin talauci (SIP) da ake zartarwa a karkashin ofishin mataimakin shugaban kasa.

A jawabin da ya yi yayin bude baki da ya gayyaci Osinbajo, Shugabannin hukumomin tsaro da shugabanin hukumomin gwamnatin tarayya a fadarsa da ke Abuja, Buhari ya shawarci Osinbajo ya yi takatsantsan game da yadda ya ke ziyartar kasuwanni.

"Na gargadi mataimakin shuganan kasa a kan 'market money'. Ba na son a kai masa farmaki musamman yadda tika-tikan mata ke zuwa suna fuskantarsa, ya kamata ya yi takatsantsan.

"Shirin na da matukar kyau kuma ya sanya talakawa da yawa sun matso kusa da gwamnati saboda N5,000 da N10,000 da aka basu a matsayin bashi."

DUBA WANNAN: Karin albashi: An gargadi 'yan kasuwa game da karin farashin kayayaki

Ba na son a kai maka farmaki, Buhari ya gargadi Osinbajo

Ba na son a kai maka farmaki, Buhari ya gargadi Osinbajo
Source: Twitter

Shugaban kasa ya koka kan yadda 'yan bokon kasar suka gaza magance matsalar rashin walwala da ilimi na talakawar kasan.

"Idan ina fita zagaye cikin gari ina matukar bakin cikin ganin halin da talakawan kasar nan ke ciki. Za ka gan kananan yara wato almajirai sanye da yagagen tufafi dauke da kwanon roba suna neman abinda za su ci.

"Suna ganin ilimi a matsayin wani gata ne na musamman. Ina tunanin a matsayin mu na 'yan bokon Najeriya muna gazawa, ina ganin ya dace mu samu shirin da zai samar da ilimi ga talakawan mu.

"Saboda haka ina maraba da shirin ciyar da 'yan makaranta da mataimakin shugaban kasa ya kaddamar. Idan ka duba garuruwan mu za ka lura adadin yaran da ke zuwa makaranta sun karu saboda ciyarwa da akeyi a makarantun. Wannan shine halin da kasar ke ciki."

"Amma wasu daga cikin mu ba su damu da halin da wasu ke ciki ba, kansu kawai suka sani," inji shugaban kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Online view pixel