Babbar mota makare da fasinja ta kama ci da wuta a jahar Legas, ta kone kurmus

Babbar mota makare da fasinja ta kama ci da wuta a jahar Legas, ta kone kurmus

Wata motar daukan fasinja a jahar Legas ta kama da wuta inda ta har ta cinye kurmus yayin da direban motar yayi kokarin kutsa kai ta gefen wata babbar motar dakon man fetir data fadi akan titi, kuma fetirin da ta dauko ya dinga kwarara a kasa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito akalla fasinjojin motar guda hudu ne suka jikkata, daga cikinsu har da direban, yayin da sauran suka tsallake rijiya da baya, sa’annan hakan ya janyo cunkoson daruruwan motoci akan gadar Afa-Isolo.

KU KARANTA: Kotu ta hana Magu ya gudanar da bincike akan Adams Oshiomole

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:30 na safiyar Talata, daidai lokacin da ma’aikata, yan makaranta da yan kasuwa suke rige rigen fita daga gidajensu zuwa wajen aiki, makaranta da kasuwa.

“Salansar motar Bus dinne ya kwakkwashi fetir daya zube ya kwanta a cikin ramukan kan hanyar, a lokacin da motar ta kama hanyar sauka daga gadar, sai salansar ta dinga gogan kwalta sakamakon gangara ne, nan take wuta ya kama ci bal bal.” Inji shi.

Shaidan, wanda yace yana gefen motar Bas din a lokacin da hadarin ya faru ya kara da cewa ba tare da bata lokaci ba aka garzaya da mutane hudun zuwa babban asibitin karamar hukumar Isolo, amma yace shima hayaki ya turnuke motarsa.

Rahotanni sun bayyana cewa tun da misalin karfe 5:15 na yamma ne tankar man ta fadi akan gadar, daga bisani jami’an bada hannu dana hukumar kashe gobara suka dauke motar daga kan hanyar, amma man ya riga ya malala zuwa cikin ramukan hanyar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel