Bani da masaniya cewa Jonathan ya cire $47m daga CBN, inji hadiminsa

Bani da masaniya cewa Jonathan ya cire $47m daga CBN, inji hadiminsa

-Dudafa ya karyata zargin da hukumar EFCC keyi masa na cewa yanada masaniya akan $47m da Jonathan ya fitar daga babban bankin Najeriya

-Hukumar ta EFCC tace an bashi wadannan kudade ne cikin wata jaka inda aka umarce shi da ya baiwa maigidansa

Tsohon hadimi na musamman ga shugaba Jonathan mai bada shawara akan lamuran cikin gida wato Waripamo-Owei Dudafa ya karyata zargin dake ake masa cewa ya karbi jakar makudan kudaden da yawansu ya kai $47m a madadin maigidansa.

Dudafa ya karyata wannan batu, kamar yadda hukumar yaki da cin hanci da kuma cin duduniyar tattalin arziki ta EFCC ke cewa Kanal Adegbe ne ya mika masa jakar domin ya baiwa Jonathan.

Bani da masaniya cewa Jonathan ya cire $47m daga CBN, inji hadiminsa

Owei Dudafa
Source: UGC

KU KARANTA:Yan bindiga sun kashe jami'an JTF 6 a Zamfara

Hadimin yace bashi da wata masaniya akan wadannan kudaden da hukumar EFCC ke ikirarin cewa an fitar dasu daga babban banki Najeriya wato CBN ta hanyar tsohon mai ba shugaban kasa shawara akan lamuran tsaro Kanal Sambo Dasuki (mai ritaya).

Wannan musayar bayanai tsakanin lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo da Dudafa ya auku ne a babbar kotun kasa dake Legas inda EFCC ke bincike wasu kudaden dake da alaka da uwargidan Jonathan wanda cikinsu akwai $8.4m da kuma N9.2bn.

Hukumar EFCC ta samu damar karbe wadannan kudade a ranar 26 ga watan Afrilun 2017 bisa amfani da hukuncin da Alkali Mojisola Olatoregun yayi.

Sai dai kuma Patience Jonathan bata gamsu da hukuncin ba inda ta daukaka kara zuwa kotu koli. Ta shigar da wannan karar ne ta hanyar manyan lauyoyinta, Ifedayo Adedipe (SAN) da kuma Mike Ozekhome (SAN).

Duk da wannan yinkurin bata samu nasara ba, hasalima kotun kolin ta nemeta da ta koma babbar kotun Legas ta gamsar dasu dalilin da yasa bata son baiwa gwamnatin tarayya wannan kudin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel