Boko Haram: Har yanzu akwai babban yanki a jihar Borno da ba a iya shiga - Osinbajo

Boko Haram: Har yanzu akwai babban yanki a jihar Borno da ba a iya shiga - Osinbajo

Mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi fashin baki da cewar kawowa yanzu akwai babban kaso na wasu yankuna da ma'aikatan lafiya ba su da damar samun shiga a jihar Borno sakamakon ta'azzarar ta'addancin kungiyar masu tayar da baya ta Boko Haram.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito a shafin ta na ranar Talata, 14 ga watan Mayun 2019, mataimakin shugaban kasa ya ce akwai al'umma da dama na jihar Borno da suka wanke kafafun su wajen tserewa zuwa wasu kasashe dake makotaka da Najeriya.

Osinbajo, sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha yayin zaman majalisar zantarwa

Osinbajo, sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha yayin zaman majalisar zantarwa
Source: UGC

Osinbajo wanda sakataren gwamnatin tarayya ya wakilta, Boss Mustapha, ya bayyana hakan ne yayin taron muhawara da karawa juna sani a kan jin kan al'ummar kasar nan da aka gudanar cikin garin Abuja a ranar Litinin.

Mataimakin shugaban kasar ya ce an ribaci taron wajen samun dama domin tunawa da rayukan mutane 74 da suka riga mu gidan gaskiya yayin yunkurin su na kai agaji kan wadanda suke cikin hali na damuwa da kuma bukatar taimakon gaggawa.

KARANTA KUMA: Kwamishinan Labarai ya sha da kyar bayan hadarin Mota a jihar Legas

Sabanin yadda ta kasance a gwamnatocin da suka shude, Farfesa Osinbajo ya ce a halin yanzu al'amurra na hanzari wajen bayar da agaji da kuma jin kan al'umma sun inganta a karkashin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel