Yanzu Yanzu: An nemi kotun zabe ta dakatar da rantsar da Buhari

Yanzu Yanzu: An nemi kotun zabe ta dakatar da rantsar da Buhari

Wata jam’iyyar siyasa, Hope Democratic Party (HDP), ta shigar da wata kara da ke neman kotun zaben Shugaban kasa tayi umurnin dakatar da rantsar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar 29 ga watan Mayu.

Jam’iyyar ta kuma nemi a hana rantsar da Shugaban alkalan Najeriya, a ranar 29 ga watan Mayu.

A wani jawabi da manema labarai suka samu a ranar Talata, 14 ga watan Mayu, jam’iyyar Hope Democratic Party ta shigar da kara akan dalilai shida daidai da sashi daya ayan na biyu a kundin tsarin mulkin 1999.

Wasu daga cikin dalilan shigar da karar shine cewa akwai wani shari’a da ke kasa wanda ke kalubalantar nasarar shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu.

Yanzu Yanzu: An nemi kotun zabe ta dakatar da rantsar da Buhari

Yanzu Yanzu: An nemi kotun zabe ta dakatar da rantsar da Buhari
Source: Facebook

Jam’iyyar tace an rigada an kai wa shugaba Buhari takardar karan sannan anyi chanjin zantuka.

Ta kara da ikirarin cewa duk da shari’an da ake akan Shugaban kasar, yana ta kokari da shirye-shiryen rantsar dashi da Shugaban alkalan Najeriya zai yi ranar 29 ga watan Mayu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu yanzu: Ribadu ya wakilci Buhari a kotun sauraron kararrakin zabe

Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa doka ta yanke cewa da zaran an dasa ayar tambaya wajen kalubalantar zaben wani toh wannan mutumin bai cancanci daukar rantsuwar kama aiki ba ko kuma hawa kujerar mulki.

An shigar da karan ne a ranar 9 ga watan Mayu sannan a yau Talata, 14 ga watan Mayu ne za a saurari shari’an.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel