Hukumar fasa kori ta Kwastam ta raba kayan abinci a Bauchi

Hukumar fasa kori ta Kwastam ta raba kayan abinci a Bauchi

- Hukumar kwastam ta tallafawa sansanin yan gudun hijira da kayan abinci a jihar Bauchi

- Wannan tallafin ya biyo bayan umarni daga babban ofishin hukumar dake Abuja na cewa a baiwa sansanin yan gudun hijira wadannan kayayyaki

- Kayayyakin da aka raba sun hada da; buhuhunan shinkafa, kwalayen taliya da kuma damin sutura ta sanyawa

A jiya Litinin, 13 ga watan Mayu hukumar fasa kauri wato kwastam ta raba kayan abinci da tufafi a sansanin yan gudun hijira dake Bauchi.

Kayayyakin da aka raba sun hada da; buhuhunan shinkafa guda 929, kwalaye taliya 30 da kuma damin sutura ta sanyawa guda 307.

Hukumar fasa kori ta Kwastam ta raba kayan abinci a Bauchi

Hukumar fasa kori ta Kwastam ta raba kayan abinci a Bauchi
Source: UGC

Shugaban hukumar mai kula da shiyyoyin Bauchi da Gombe , Kalla Hamis shine ya bayyana wannan labari ranar Litinin ga yan jarida a babban ofishin shiyyar dake Bauchi.

KU KARANTA:Bamu ba kungiyar Miyetti Allah ko kwabo ba – Gwamnatin tarayya

“ Mun samu umarni daga babban ofishin hukumarmu na kasa cewa mu bayar da wadannan kayayyaki zuwa ga sansanin yan gudun hijira na Bauchi.

“ Wadannan kayayyakin kuma sun hada da; buhun shinkafa 929, kwalin taliya 30, da kuma damin sutura guda 307 wadanda babbar kotun kasa ta karbe tareda mallakama gwamnatin tarayya.” Inji shi.

A labari mai kama da wannan, zaku ji cewa gwamnatin tarayya ta karyata batun cewa ta baiwa kungiyar Miyetti Allah kudi a wata tattaunawa da ta gudana tsakaninsu a jihar Kebbi.

Ministan harkokin cikin gida Abdurrahman Dambazau ne yayi wannan bayani yayinda da yake amsa tambayoyin manema labarai a ziyarar da ya kai jihar Zamfara. Ministan yae sam wanan maganar ba gaskiya bace hasalima taron yayi magana ne akan sha'anin tsaro da kuma a yankin na arewacin Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel