Sama da mutane dubu 500 ne suka cika aikin Kwastan

Sama da mutane dubu 500 ne suka cika aikin Kwastan

- Aikin da ake bukatar mutum dubu uku da dari biyu sai gashi sama da mutane dubu dari biyar sun cika

- Duk da haka dai hukumar ta ce za ta yi iya bakin kokarin ta wurin ganin ta yi adalci wurin daukin ma'aikatan

Hukumar Kwastam ta kasa ta ce akalla mutane 524,315 suka samu nasarar kamalla cika aikin da suka bayyana cewa zasu dauki ma'aikata mutum 3,200.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Mista Joseph Attah shi ne ya bayyana haka ga kamfanin dillancin labarai na Najeriya jiya Litinin a Abuja.

Idan ba a mance ba a ranar 17 ga watan Afrilu, 2019, majiyar mu LEGIT.NG ta kawo muku rahoton cewa hukumar ta bude shafinta na yanar gizo domin daukar ma'aikata mutum 3,200.

Sama da mutane dubu 500 ne suka cika aikin Kwastan
Sama da mutane dubu 500 ne suka cika aikin Kwastan
Source: UGC

Hukumar ta ce za ta dauki kimanin mutane 800 a matsayin manyan ofisoshi, da kuma mutane 2,400 a matsayin kananan ofisoshi.

Attah ya shaidawa kamfanin dillancin labarai cewa kimanin mutane 278,582 suka cika matsayin Superitendent Cadre, yayin da sauran mutanen suka cika matsayin Inspectorate da kuma Assistant Cadres.

KU KARANTA: Sarakunan gargajiya sun bukaci a rufe hanyoyin sadarwa a jihar Zamfara

"Kimanin mutane 828,333, suka cika aikin amma baa duka bane suka samu damar kammalawa," in ji shi.

Mai magana da yawun hukumar ya tabbatar da cewa hukumar za ta yi adalci wurin daukar ma'aikatan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng

Online view pixel