Sarakunan gargajiya sun bukaci a rufe hanyoyin sadarwa a jihar Zamfara

Sarakunan gargajiya sun bukaci a rufe hanyoyin sadarwa a jihar Zamfara

- Sarakunan gargajiyan jihar Zamfara sun bukaci gwamnatin tarayya ta dakatar da kafafen sadarwar wayar tarho a fadin jihar domin kawo karshen ta'addanci a jihar

- Sun bayyana cewa hakan zai taimaka matuka wurin dakile ta'addanci a jihar

Majalisar sarakunan gargajiya ta jihar Zamfara ta bukaci gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin bincike akan wadanda suke da hannu a kashe-kashen jihar, domin hukunta su.

Shugaban majalisar Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Ahmad, shine ya yi rokon jiya Litinin a lokacin da ya karbi bakuncin ministan cikin gida, Abdulrahman Dambazau (Rtd.), a fadarsa.

"Ba za mu taba yafewa mutanen da suke da hannu a kashe-kashe da raba mutane wadanda ba su ji ba su gani ba da gidajen su.

Sarakunan gargajiya sun bukaci a rufe hanyoyin sadarwa a jihar Zamfara

Sarakunan gargajiya sun bukaci a rufe hanyoyin sadarwa a jihar Zamfara
Source: Depositphotos

"Kafa kwamitin zai taimaka wurin hukunta duk wadanda aka kama da hannu a rikicin," in ji shi.

Sarkin ya yaba da matakan da aka dauka akan 'yan ta'addar, irin su rufe duk wata hanya da za su samu abinci, ya kara da cewa hakan ba karamin tasiri ya yi akan 'yan ta'addar ba.

"Ya kamata a rufe duk wata hanyar wayar tarho a jihar nan, saboda sai da wayar tarho 'yan ta'addar suke iya kiran iyalan wadanda suka kama su bukaci kudi.

KU KARANTA: Garin dadi da nisa: Wani sarki ya saka doka akan mazajen kasarsa da su dinga auren mata a kalla guda hudu

"Idan aka rufe kafar sadarwar tarho a jihar nan na tsawon watanni uku zuwa shida, hakan zai taimaka sosai, saboda ko masu leken asiri ga 'yan ta'addar baza su samu damar kai musu rahoto ba."

Sarkin ya ce bayan rufe hanyoyin sadarwa, ya kamata aa rufe duk wasu hanyoyi da 'yan ta'addar suke bi, sannan a kama duk wani mutum da aka ga ya biyo hanyar.

Sarkin ya ce yanzu babu sauran rikincin makiyaya da manoma a cikin jihar, kawai 'yan ta'adda ne suke cin karen su ba babbaka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel