Yanzu yanzu: Ribadu ya wakilci Buhari a kotun sauraron kararrakin zabe

Yanzu yanzu: Ribadu ya wakilci Buhari a kotun sauraron kararrakin zabe

Shugaban Hukumar Yaki da masu yiwa arzikin kasa ta'annti, EFCC Mallam Nuhu Ribadu ya hallarci zaman shari'a da ake gudanarwa a kotun saurarakon kara a Abuja.

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Hope Democratic Party, Ambrose Awuru ne ya shigar da kara a kan shugban kasa Muhammmadu Buhari.

A lokacin da alkalin kotun ya kira lauyan Shugaba Muhammadu Buhari sai Ribadu wanda jigo ne a jam'iyyar APC ya sanar da cewa shine zai wakilci shugaba Muhammadu Buhari wanda Awuru ke kallubalantar nasarar da ya samu a zaben ranar 23 ga watan Fabrairu.

Yanzu yanzu: Ribadu ya wakilci Buhari a kotun sauraron kararrakin zabe

Yanzu yanzu: Ribadu ya wakilci Buhari a kotun sauraron kararrakin zabe
Source: UGC

DUBA WANNAN: Karin albashi: An gargadi 'yan kasuwa game da karin farashin kayayaki

Dare Oketade shine lauya da ke kare jam'iyyar APC a kotun.

Direktan fannin shari'a na Hukumar zabe mai zaman kanta INEC, Oluwatoyin ne ya wikilci INEC.

Cif Wole Olanipekun (SAN) ne ya jagoranci kauyoyin da ke kare Buhari yayin da Lateef Fagbemi (SAN) ya jagoranci tawagar lauyoyin jam'iyyar APC.

Bayan wannan karar, wasu jam'iyyun siyasa uku sun shigar da karar kallubalantar zaben shugaba Muhammadu Buhari ciki har da Atiku Abubakar dan takarar jam'iyyar PDP.

A halin yanzu Justice Zainab Bulkachuwa ne jagorantar alkalai biyar da ke sauraron karar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel