Bamu ba kungiyar Miyetti Allah ko kwabo ba – Gwamnatin tarayya

Bamu ba kungiyar Miyetti Allah ko kwabo ba – Gwamnatin tarayya

Gwamnatin Tarayya bata baiwa kungiyar Miyetti Allah kudi ba a lokacin tattaunawarta da kungiyan a Birnin Kebbi, ministan harkokin cikin gida Laftanal Janar Abdulrahman Danbazau, ya bayyana haka a ranar Litinin, 13 ga watan Mayu.

Ministan yayi maganan ne a Anka, jihar Zamfara, a ranar Litinin yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai.

Ministan a baya ya fada ma sarkin Anka, Alhaji Attahiru Ahmad cewa ya zo jihar ne a madadin shugaban kasa Muhammadu Buhari don maganta rashin tsaro a jihar.

Ya ba manoma tabbacin cewa gwamnati zata samar da isasshen tsaro gare su a lokacin ayyukan noma a lokacin rani.

Bamu ba kungiyar Miyetti Allah ko kwabo ba – Gwamnatin tarayya

Bamu ba kungiyar Miyetti Allah ko kwabo ba – Gwamnatin tarayya
Source: Depositphotos

Ahmad, wanda ya kasance shugaban kungiyar masu sarauta a jihar, ya bukaci gwamnati da ta kara kwazo don ganin an magance rigingimu.

Ya ce har sai an dauki mataki mai tsanani, baza a gudanar da ayyukan noma ba a jihar a shekaran nan, ya kara da cewa yawancin al’umman kauyuka sun yi gudun hijira daga kauyukan su, har yawancin mata da yara sun koma da zama a birane.

KU KARANTA KUMA: Idan mutum yace zai dunga sauraran majalisar dattawa, kwakwalwar sa ko zata buga – El-Rufai

Ahmad yace a wannan lokacin, akwai fiye da mutane 16,000 wadanda suka balle daga asalinsu a Anka bayan sun kubuta daga hare-haren yan bindiga a kayyuka.

Ya ba da shawarar cewa jami’an tsaro su shiga kauyukan da mazauna suka bari wanda ya zamo mafaka ga yan bindiga don baiwa masu gudun hijira dawowa gida.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel