Patience Jonathan ta kasance tana daukan albashi 700k a wata duk da ta bar aiki - EFCC

Patience Jonathan ta kasance tana daukan albashi 700k a wata duk da ta bar aiki - EFCC

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) a ranar Litinin, 13 ga watan Mayu tayi zargin cewa Dame Patience Jonathan, uwargidar tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ta ci gaba da karban albashinta na N700, 000 duk wata, watanni bakwai bayan tayi ritaya a matsayin ma’aikaciyar gwamnati.

An tattaro cewa tsohuwar uwargidar Shugaban kasar, wacce tayi ritaya daga ma’aikatar gwamnatin Bayelsa a matsayin sakatariyar din-din-din a ranar 14 ga watan Oktoba, 2014 ta ci gaba da karban albashi har zuwa watan Mayun 2015, lokacin da mijinta ya bar kujerar mulki.

Hukumar ta bayyana hakan a gaban babbar kotun tarayya da ke Lagas a lokacin zaman shari’a na kwace dukiyar uwargidar Jonathan da ke gaban kotun.

Hukumar na rokon kotun da ta yi umurnin kwace wasu kadarori na $8.4 million da naira biliyan 7.4 na karshe da ake zargin mallakinta ne.

Patience Jonathan na ta karban albashin N700,000 tsawon watanni bayan tayi ritaya – EFCC

Patience Jonathan na ta karban albashin N700,000 tsawon watanni bayan tayi ritaya – EFCC
Source: Twitter

Justis Mojisola Olatoregun taki amincewa da bukatar EFCC na kwace dukiyoyi amma ta umurci bangarorin da su bayar da hujja na fatar baki domin tabbatar da mammalakin kadarorin.

Tace akwai sarkakiya a karar da ke gabanta, inda ta kara da cewa akwai bukatar hujja ta fatar baki domin wanke su.

KU KARANTA KUMA: Idan mutum yace zai dunga sauraran majalisar dattawa, kwakwalwar sa ko zata buga – El-Rufai

A ranar 20 ga watan Afrilu da ya gabata ne alkalin tayi umurnin mallaka wa gwamnatin tarayya kadarorin na wucin-gadi.

An dage sauraron shari’an zuwa ranar 24 ga watan Mayu da misalin karfe 11 na safe.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel