Idan mutum yace zai dunga sauraran majalisar dattawa, kwakwalwar sa ko zata buga – El-Rufai

Idan mutum yace zai dunga sauraran majalisar dattawa, kwakwalwar sa ko zata buga – El-Rufai

Gwamna Nasir E-Rufai ya yi watsi da hasashe majalisar dattawan Najeriya da ke cewa babbar titin Abuja zuwa Kaduna ne hanya mafi hatsari a kasar, cewa a yanzu hanyar yayi kyau kuma matafiya na iya bi.

El-Rufai ya bayyana hakan ne a lokacin da yayi jawabi ga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan wata ganawar sirri da yayi da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Shugaban kasa.

Majalisar dattawa a ranar 8 ga watan Mayu ta bayyana babbar titin Abuja zuwa Kaduna a matsayin hanya mafi hatsari a Afrika saboda ayyukan masu garkuwa da mutane da yan fashi da makami da ke aiki a hanyar.

Gwamnan ya bayyana cewa ba kasafai bane mutum zai damu da sauraren muhawaran ‘yan majalisar dattawan Najeriya.

Idan mutum yace zai dunga sauraran majalisar dattawa, kwakwalwar sa ko zata buga – El-Rufai

Idan mutum yace zai dunga sauraran majalisar dattawa, kwakwalwar sa ko zata buga – El-Rufai
Source: Twitter

Ya kara da cewa tatsuniyoyi kawai suke shirgawa a majalisar da idan ka ce zaka saurare su tabbas kwakwalwar ka zai iya buga wa.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa Buhari bai sanya baki a rigimar masarautar Kano ba

Ya jadadda cewa shi dai bai san da wani ma’auni sanatocin suka yi nasu gwajin ba domin jami’an tsaro suna aiki matuka wajen ganin an kau da wadannan miyagun mutane a wannan hanya.

“Titin Kaduna zuwa Abuja yayi kyau yanzu, jami’an tsaro na aiki ba dare ba rana a wannan titi, abinda zan iya fadi kenan. Amma wasu sun taru a wani zaure suna fadin abinda ba haka ba."

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel