Kwamishinan Labarai ya sha da kyar bayan hadarin Mota a jihar Legas

Kwamishinan Labarai ya sha da kyar bayan hadarin Mota a jihar Legas

- Wani kwamishinan gwamna Akinwunmi Ambode ya tsallake rijiya da baya bayan aukuwar hatsari mota akan hanyar sa ta dawowa daga gona

- Kwamshina Kehinde Bamigbetan ya ce hatsarin ya auku a sanadiyar gyangyadi da ya dauki direban sa

- Duk da samun munanan raunuka, Kehinde ya yi godiya ga Mahallici da ya tsaretar da rayuwar su

Kwamishinan labarai na gwamnatin jihar Legas, Kehinde Bamigbetan tare da direban sa, a ranar Lahadin da ta gabata sun tsallake rijiya da baya biyo bayan aukuwar wani mummanan tsautsayi na hatsarin mota.

Kwamishinan Labarai na jihar Legas, Kehinde Bamigbetan

Kwamishinan Labarai na jihar Legas, Kehinde Bamigbetan
Source: Facebook

Kwamishinan Labarai na jihar Legas, Kehinde Bamigbetan tare da raunukan sa

Kwamishinan Labarai na jihar Legas, Kehinde Bamigbetan tare da raunukan sa
Source: Facebook

Bamigbetan wanda ya kasance tsohon shugaban karamar hukuma gabanin samun nadin mukamin kujerar kwamishina a gwamnatin jihar Legas karkashin jagorancin Gwamna Akinwunmi Ambode, ya samu munanan raunuka a yayin da mai aukuwar ta auku.

Yayin labarta yadda tsautsayin ya auku, Bamigbetan ya ce gyangyadi da ya dauki direban motar sa yayi sanadiyar gwabzawa wata babbar motar makaman yaki inda nan take suka yi kuli-kulin-kubura.

KARANTA KUMA: Boko Haram: Gana ya hana zaman lafiya a kananan hukumomi 3 na jihar Benuwai - Ortom

Bayan samun munanan raunuka daban-daban yayin aukuwar hatsarin akan hanyar su ta dawowa daga wata gona, Kwamishina Bamigbetan ya yi godiya ga Mai Duka da ya yi masu jinkiri na tsawaita nisan kwanakin su a doron kasa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel