Boko Haram: Gana ya hana zaman lafiya a kananan hukumomi 3 na jihar Benuwai - Ortom

Boko Haram: Gana ya hana zaman lafiya a kananan hukumomi 3 na jihar Benuwai - Ortom

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai a ranar Litinin da ta gabata ya bayyana cewa, Terwase Akwaza, wanda ya shahara da sunan Gana, ya hana zaman lafiya tare da muzgunawa al'umma cikin wasu kananan hukumomi uku na jihar.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, gwamna Samuel ya bayyana hakan ne yayin ganawar sa ta sirrance da shugaban kasa Muhammadu Buhari cikin fadar Villa dake garin Abuja a ranar da ta gabata.

Gwamna Ortom tare da shugaban kasa Buhari cikin fadar Villa

Gwamna Ortom tare da shugaban kasa Buhari cikin fadar Villa
Source: Twitter

Gwamnan yace Gana wanda ya samu horaswa a hannun kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram, ya ci gaba da addabar al'ummar wasu yankunan jihar Benuwai da kuma na makociyar jiha ta Taraba.

Yayin hikaito miyagun ababe na ta'ada da suka hadar da garkuwa da mutane, fashi da makami da kuma zubar jinin al'umma ba tare da hakki ba, gwamna Ortom ya ce Gana ya assassa zaman dar-dar a wasu kananan hukumomi na Katsinan-Ala, Logo da kuma Ukum da jihar Benuwai kunsa.

KARANTA KUMA: Zababben Gwamnan Gombe ya kafa kwamitin mutum 30 na karbar ragamar mulki

Dangane da rikicin makiyaya da manoma, gwamna Ortom ya ce an samu wanzuwar zaman lafiyar daidai gwargwado a sakamakon wadatattun wuraren kiwo da gwamnatin jihar ta bayar da dama ko wane mabukaci ya samar wa kansa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel