Talauci: Da kyar Osinbajo ya samu na yarda da Trader Moni - Shugaba Buhari

Talauci: Da kyar Osinbajo ya samu na yarda da Trader Moni - Shugaba Buhari

Mun samu labari cewa shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna takaicinsa game da halin talauci da rashin ilmin da da-yawa daga cikin mutanen kasar nan su ke fama da ita a halin yanzu.

Kamar yadda mu ka samu labari, shugaban kasar ya bayyana wannan ne a lokacin da yayi buda-bakin azumi tare da mataimakinsa watau Farfesa Yemi Osinbajo, da Ministocin kasar da kuma sauran manyan gwamnati da Hafsoshin tsaro.

Shugaban kasar ya bayyana cewa talaucin da yayi wa mutane katutu a Najeriya, yana fusata sa. Shugaba Buhari yayi kira ga manyan kasar da su tashi tsaye wajen ganin sun yi wani abu na rage talaucin da yayi wa mutane mugun kamu.

Shugaban ya kuma yabawa Yemi Osinbajo da ya kawo manufofi irin su Trader Moni da ciyar da ‘yan makaranta da su ka taimaka wajen rage radadin talauci a kasar. Buhari ya nuna cewa da farko, da bai amince da wannan tsari da aka kawo ba.

KU KARANTA: Mun ga amfanin tsare-tsaren N-power, da TraderMoni – Gwamnan APGA

Buhari ya kara da cewa a duk lokacin da ya ga kananan yara da barkakkun tufafi su na yawon bara da kwanon roba, su na neman abinci, ya kan ji ran sa ya baci. Shugaban kasar yace ya kamata gwamnati ta rika ba kowa ilmi a fadin kasar nan.

Shugaban kasar ya kuma yi magana a kan yadda Ministoci su kayi ta fama da dogon taro a makon da ya gabata, duk da cewa ana azumi. Buhari yake cewa za a sake rantsar da shi ne a cikin Azumi don haka dole ya tuna da alkawarun da yayi.

Daga cikin wadanda su ka sha ruwa tare da shugaban kasar akwai gwamnan CBN, Godwin Emefiele, Darektan NTA, Alhaji Yakubu Ibn Muhammed, da shugaban hukumar Alhazai na kasa, Abdullahi Mukhtar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel