Matsalar tsaro: Yaci ace Buhari ya fatattaki ministan tsaro – Inji Sarkin Zamfara

Matsalar tsaro: Yaci ace Buhari ya fatattaki ministan tsaro – Inji Sarkin Zamfara

Shugaban majalisar sarakunan jahar Zamfara, Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Ahmad ya bayyana cewa tun tuni ya kamata ace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fatattaki ministan tsaro, Mansur Dan Ali duba da tabarbarewar tsaro a jahar Zamfara.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sarki Attahiru ya bayyana haka ne a matsayin martani game da zargin da Ministan tsaro Mansur Dan Ali yayi na cewa wai da akwai hannun Sarakunan gargajiya a cikin kashe kashen da ake fama dashi a jahar Zamfara.

KU KARANTA: Yaki da ta’addanci: Mayakan Boko Haram sun kashe manyan kwamandojin Soji guda 2

Matsalar tsaro: Yaci ace Buhari ya fatattaki ministan tsaro – Inji Sarkin Zamfara

Sarkin Anka da Mansur
Source: UGC

Da wannan ne basaraken yake ganin wannan zargi yana da nauyi sosai, don haka ya shawarci Ministan a matsayinsa na dan asalin karamar hukumar Birnin Magaji daya koma garin domin yaki da yan bindigan.

“Abin takaici ne ace Ministan ya zargemu da hannu cikin matsalar tsaro ta hanyar taimaka ma yan bindiga, da a wata kasa muke da tuni an sallameshi daga aiki saboda wannan babban zargi, amma mun yi shiru ne saboda shi danmu ne, kaje garinsu kaga halin da ake ciki.” Inji shi.

Sai dai a hannu guda kuma Sarkin ya jinjina ma gwamnatin tarayya da karin Sojojin data tura jahar Zamfara don yaki da bindiga, amma yace akwai bukatar kara adadin Sojojin dake kan duwatsun garin Anka, tare da basu isassun kayan aiki irin na zamani.

Daga karshe Sarkin yayi kira ga gwamnati data tashi haikan kan matsalar yan bindiga da masu satar mutane, saboda yace suna samun makudan kudade daga masu biyan kudin fansa, kuma dasu suke amfani wajen sayen makamai da sauransu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel