Yadda mu kayi da Shugaba Buhari da na je ofishinsa – Gwamnan Anambra Obiano

Yadda mu kayi da Shugaba Buhari da na je ofishinsa – Gwamnan Anambra Obiano

Gwamna Willie Obiano na jihar Anambra ya bayyana yadda zaman sa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kasance jiya. A Ranar Litinin dinnan ne manyan su ka sa labule a fadar Aso Villa.

Willie Obiano yake cewa ya jinjina gwamnatin shugaba Buhari a kan yadda manyan ayyukan hanyoyi irin su titin Onitsha zuwa Awka da kuma Gadar 2nd Niger su ke tafiya. Gwamnan ya kuma yaba da sauran tsare-tsaren gwamnatin nan.

Gwamnan ya bayyana wannan ne a lokacin da ya hadu da manema labarai a Ranar 13 ga Watan Mayu a fadar shugaban kasa. Gwamna Obiano yake cewa ya nemi shugaba Buhari ya karo kawo tsare-tsaren inganta rayuwa cikin jihar Anambra.

Obiano yake kuma cewa yayi kira ga shugaban kasa da ya kara dagewa wajen ganin gwamnatinsa tayi wa jihar Anambra ayyukan more rayuwa. Babban gwamnan na jam’iyyar APGA yake cewa sai a Ranar ya gana da Buhari tun da ya lashe zabe.

KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari ya gana da wasu manyan Gwamnoni 3

Yadda mu kayi da Shugaba Buhari da na je ofishinsa – Gwamnan Anambra Obiano

Gwamnan Anambra ya yaba da aikin Gwamnatin Shugaba Buhari
Source: Depositphotos

A cewar gwamnan, ya kira Buhari bayan ya samu nasara a zaben da aka yi bana, sai jiya kuma ya samu ganin sa. Bayan haka, gwamnan yake cewa yayi magana da shugaban kasa a kan nadin Ministoci da sauran mukamai daga jihar Anambra.

Cif Obiano yake cewa wasu titunan jihar sun sukurkuce don haka ya nemi Buhari, wanda shi ne ya gina su a lokacin yana PTF da ya taimaka ya gyara wadannan hanyoyi. Gwamnan yana kuma neman Buhari ya rika damawa da mutanen Anambra.

A jawabin na gwamnan, ya bayyana cewa tsare-tsaren N-power, da TraderMoni da kuma ciyar da ‘Yan makaranta da wannan gwamnati ta ke yi, yayi amfani ainun, fiye da yadda aka yi tunani da farko.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel