Yaki da ta’addanci: Mayakan Boko Haram sun kashe manyan kwamandojin Soji guda 2

Yaki da ta’addanci: Mayakan Boko Haram sun kashe manyan kwamandojin Soji guda 2

Akalla dakarun rundunar Sojin Najeriya ne suka gamu da ajalinsu a yayin da wata nakiya da mayakan Boko Haram suka binne akan hanya ta tashi a ranar Litinin, 13 ga watan Mayu, yayin da wasu guda hudu suka samu munanan rauni.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito daga cikin wadanda suka mutu akwai kwamandojin rundunar Sojan kasa guda biyu, guda daga cikinsu mai mukamin Laftanar kanal, tare da direbansa da kuma dogarinsa.

KU KARANTA: Yansanda sun ceto mutane 2 daga hannun masu garkuwa, sun kama miyagu 3

Majiyar ta kara da cewa harin ya faru ne a daidai lokacin da Sojojin runduna ta 145 suke gudanar da aikin sintiri ne da misalin karfe 9:30 na safiyar Litinin akan hanyar Mauli zuwa Borgozo a jahar Borno.

Sai dai ba tare da wata wata ba aka tura Sojoji domin su kwaso gawarwakin wadanda suka mutu, tare da ceto wadanda suka jikkata, daga cikin kayan aikin Sojojin da harin ya shafa akwai motocin yaki guda biyu da kuma motar daukan Sojoji kirar Tata.

Wannan hari na daga cikin hare haren da suka sabbaba asara ga rundunar Sojan kasa tun shekarar 2009 da aka fara yaki da kungiyar Boko Haram, don kuwa a kimanin watanni shida da suka gabata sai da yan ta’adda suka kashe Laftanar Kanal Ibrahim Sakaba a wani hari a Matele, jahar Borno.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel