Satar mutane: Hanyar Kaduna-Abuja tayi lafiya – El-Rufai ga matafiya

Satar mutane: Hanyar Kaduna-Abuja tayi lafiya – El-Rufai ga matafiya

Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya karyata wani rahoto daya fito daga majalisar dattawan Najeriya dake cewa wai hanyar Kaduna zuwa Abuja ce hanya mafi hatsari a duk fadin Najeriya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da yan jaridu bayan wata ganawar sirri da yayi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar gwamnatin Najeriya, inda yace jama’a su rabu da batun majalisa, hanyar Kaduna tayi lafiya, a cewarsa.

KU KARANTA: Tarin motocin alfarma: Me zaka fada ma Allah – Gudaji Kazaure ya tambayi Dino Melaye

Idan za’a tuna a ranar 8 ga watan Mayu ne majalisar dattawan Najeriya ta bayyana hanyar Kaduna zuwa Abuja a matsayin hanyar da tafi hatsari a duk nahiyar Afirka sakamakon yawan sace sacen matafiya da yan bindiga suke yi akan hanyar.

Sanatan Kaduna, Shehu Sani ne yayi wannan ikirarin a gaban majalisar inda yace hanyar na daga cikin hanyoyi mafi hatsari a Afirka, yayin da Sanata James Manager daga jahar Delta yace ba wai hanyar na daga cikin mafi hatsari bane, a’a, itace mafi hatsari a Afirka.

Sai dai El-Rufai ya mayar musu da kakkausar suka, inda yace “Idan kana yarda da duk abinda ya fito daga majalisar dattawa, tabbas zaka iya samun matsalar tabin hankali, akwai abubuwan da suke fada wanda shaci fadi ne kawai.

“Ban san inda suka samu alkalumman da suka nuna musu cewa hanyar Kaduna tafi kowacce hatsari a Afirka ba, nafi son ayi magana da hujja, amma dai duk abinda wani ya fada game da hanyar a makon data gabata, a yanzu dai hanyar tayi lafiya, kuma zamu cigaba da tabbatar da tsaro a hanyar.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel