JAMB ta mayar da N5bn asusun gwamnatin tarayya

JAMB ta mayar da N5bn asusun gwamnatin tarayya

Mun samu cewa hukumar shirya jarrabawar neman shiga jami'o'i ta Najeriya JAMB, ta sake mayar da Naira biliyan biyar cikin asusu na baitul malin gwamnatin tarayya kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Hukumar JAMB a shekarar 2018 da ta gabata ta yi fifikon kwazo tsimi da tanadi na mayar da Naira biliyan takwas cikin asusun gwamnatin tarayya.

Dalibai yayin zana jarrabawar JAMB a bana
Dalibai yayin zana jarrabawar JAMB a bana
Source: Depositphotos

Babban jami'in yada bayanai na hukumar Dakta Fabian Benjamin, shi ne ya bayar da shaidar hakan yayin ganawar sa da manema labarai cikin babban birnin kasar nan na tarayya a ranar Litinin.

A sanadiyar wannan kwazo na tsimi da tanadi a bana, gwamnatin tarayya ta umurci hukumar JAMB da ta yi amfani da Naira biliyan biyu cikin biyar da ta mayar baitul malin kasa domin bunkasa harkokin ta na gudanarwa.

KARANTA KUMA: Saraki ya bayar da gudunmuwar Janareto 2 ga jami'ar Kamaldeen a Ilorin

Kamar yadda Dakta Benjamin ya bayyana, a sakamakon rage kudin sayan fam ga dalibai masu neman zana jarrabawa, hukumar JAMB ta yi tsimi da tanadin Naira biliyar a bana sabanin yadda ta mayar da Naira biliyan takwas cikin asusun gwamnati a bara.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, kwanaki biyu da suka gabata ne hukumar JAMB ta saki sakamakon jarrabawar dalibai miliyan 1.7 cikin miliyan 1.8 da suka zana a bana.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel