Abinda zanyi a matsayina na shugaban taron gangamin majalisar dinkin duniya (UNGA) –Tijjani Bande

Abinda zanyi a matsayina na shugaban taron gangamin majalisar dinkin duniya (UNGA) –Tijjani Bande

-Dan takarar shugabancin majalisar dinkin duniya yace zai mayar da hankali akan hadin kasashe dake karkashin majalisar idan ya kasance a zabe shi

-Bayan tattaunawa ta tsawon sama da sa'o'i uku Tijjani Muhammad Bande ya samu goyon bayan wakilai da suka fito daga sauran kasashen duniya

Ambasada Tijjani Muhammad Bande ranar Litinin a birnin New York dake kasar Amurka ya bayyana cigaban da zai kawo musamman fannin karfafa alaka tsakanin kasashe idan har aka zabe shi a matsayin shugaban taron gangamin majalisar dinkin duniya.

Muhammad Bande wanda shine yake wakiltar Najeriya a majalisar dinkin duniya yayi wannan karin hasken ne yayinda yake zantawa da masu ruwa da tsaki akan takararsa a shelkwatar majalisar dinkin duniya.

Abinda zanyi a matsayina na shugaban majalisar dokoki ta dinkin duniya (UNGA) –Tijjani Bande

Farfesa Tijjani Bande
Source: UGC

KU KARANTA:Ba mu da masaniya a kan kwace gidajen Saraki - EFCC

Yace matsalolin ta’addanci, talauci, rashin tsaro, yinwa da dai sauransu za’a iya kawo karshensu ne ta hanyar hadin kai tsakanin kasashe.

Wannan ya sanya kasashen dake karkashin majalisar dinkin duniya na da bukatar kasancewa tsintsiya madaurinki guda. Ganin cewa majalisar nada ikon kawo sauyi mai matukar amfani akan ababen dake damun jama’a a yau.

Dan asalin kasar Najeriyan wanda a halin yanzu shi daya tilo ke takarar zama shugaban majalisar, yace shugabancinsa zai dora akan inda shugaban da ya gabata ya tsaya tare kuma da kawo wasu sabbin kudurori domin samar da cigaba.

Ya sake bayyana cewa, shugabancinsa zai maida hankali wajen cigaba da kawo zaman lafiya a fadin duniya da kuma tsaro, saboda wannan shine abu na farko cikin jerin ababen da majalisar dinkin duniya ta damu dasu kwarai da gaske.

Kamfanin dillacin labarai na kasa wato NAN ya ruwaito cewa, an kwashe sama da sa’o’i uku ana wannan tattaunawa yayinda wakilai daga kasashen Amurka, Kanada, Kungiyar kasashen turai, Afrika ta kudu, Ghana da sauransu suka nuna goyon bayansu ga dan takarar wanda ya fito daga Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel