Sanatan Kaduna ya maidawa Shugaba Buhari martani a game da batun Digiri

Sanatan Kaduna ya maidawa Shugaba Buhari martani a game da batun Digiri

- Sanata Shehu Sani sam bai yi na’am da maganar da Buhari yayi ba

- ‘Dan Majalisar yace har yanzu Yaran masu kudi su na samun aiki

Mun samu labari cewa Sanata Shehu Sani mai wakiltar Yankin mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ya tofa albarkacin bakinsa a game da maganar da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a kan Digiri kwanan nan.

‘Dan majalisar wanda yayi fice ya bayyana cewa Yaran Talakawa ne su ke wahalar samun aikin yi a Najeriya, inda yace akwai wasu shafaffu da mai watau Yaran manya da samun aiki yake zuwan masu cikin ruwan sanyi har gobe

Sanatan na jihar Kaduna yana maida martani ne a kan kalaman shugaba Buhari inda yace a halin yanzu Digiri ba shi bane ke nuna tabbacin mutum zai samu aiki a Najeriya. Sanatan yayi gardama ne a shafinsa na Tuwita a jiya Litinin.

KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari ya sasanta rikicin Ministansa da Ma'aikata

Sanatan Kaduna ya maidawa Shugaba Buhari martani a game da batun Digiri
Shehu Sani mai rajin kare hakkin marasa karfi a zauren Majalisa
Source: Twitter

Shehu Sani ya fito shafin na sa na sada zumunta a Ranar Litinin 13 ga Watan Mayu, yana cewa Digirin da ba a iya samawa mutum abin yi da shi a Najeriya, shi ne wanda Yaron Talaka yayi, amma yace Yaran masu kudi su na samun aiki.

A shafin na sa, ‘dan majalisar ya kuma bayyana cewa kwanan nan na za a maida Makarantar nan ta Kaduna Polythechnic ta koma jami’a. ‘Yan majalisar tarayya su na aikin ganin babbar Makaranta ta zama Jami’ar Kaduna City.

Sanata Sani ya bayyana cewa a cikin ‘yan kwanakin nan Majalisa za ta mikawa shugaban kasa kudirin da zai maida makarantar koyon aikin ta zama wata babbar jami’a. Wannan zai taimaka wajen karuwar masu Digiri a Kaduna da kewaye.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Online view pixel