Ba mu da masaniya a kan kwace gidajen Saraki - EFCC

Ba mu da masaniya a kan kwace gidajen Saraki - EFCC

A ranar Lahadi ne jaridar Legit.ng ta kawo labarin cewar jaridar Punch dake fitowa kowacce ranar Lahadi ta wallafa rahoton cewar hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta kwace wasu gidaje mallakar shugaban majalisar dattijai mai barin gado, Bukola Saraki.

Jaridar ta ce gidajen da aka kwace su ne masu lamba 15a, 15b da 17 dake kan titin Macdonald a unguwar Ikoyi a cikin kwaryar birnin garin Legas.

Sai dai, a ranar Litinin, mahukunta a hukumar EFCC sun ce basu da masaniya a kan labarin dake yawo a gari dangane da garkame wasu gidajen Saraki a garin Legas.

Mukaddashin shugaban sashen yada labarai da sanarwa na hukumar EFCC, Mista Tony Orilade, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a Abuja cewar bashi da masaniya a kan batun.

"Babu wanda ya sanar da ni; a saboda haka bani da wani bayani a kan lamarin." a cewar Orilade.

Ba mu da masaniya a kan kwace gidajen Saraki - EFCC

Gidajen Saraki da tambari hukumar EFCC
Source: Twitter

Tuni Saraki, a cikin wata sanarwa da Yusuph Olaniyonu, mai bashi shawara a bangaren kafafen sadarwa, ya bayyana cewar hukumar EFCC na yi masa bita da kulli ne domin daukan fansa irin ta siyasa amadadin iyayen gidan su dake gwamnati.

Wani dan uwan Saraki, da ya bukaci a boye sunan sa, ya ce hukumar EFCC ta garkame gidajen ne ranar juma'a.

DUBA WANNAN: Rundunar Abba Kyari ta samu gagarumar nasara a kan masu garkuwa da mutane a hanyar Abuja (Hotuna)

Ya bayyana cewar hukumar EFCC ta dade da fara bincike a kan kadarori da kudaden da Saraki ya mallaka.

A lokacin da EFCC ta gurfanar da shi a shekarar 2016 a gaban kotun da'ar ma'aikata, EFCC ta shaida wa kotun cewar Saraki ya mallaki wasu gidaje a kan titin Macdonald a unguwar Ikoyi dake birnin Legas, amma tayi zargin cewar bai bayar da cikakken adireshin su ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel