CBN ya gaza wanke babban Gwamna daga zargin badakala

CBN ya gaza wanke babban Gwamna daga zargin badakala

Babban bankin Najeriya na CBN ya samu kan-sa cikin tsaka-mai-wuya wajen yin watsi da rahotannin da ke yawo na cewa an wawuri wasu kudi har Naira Biliyan 500 na wasu masu hannun jari daga bankin.

Bankin na CBN ya karyata cewa akwai wasu makudan kudi da su ka bace daga asusunsa. Bankin ya karyata wannan ne ta bakin Kakakinsa Isaac Okorafor. Okorafor ya musanya cewa akwai wasu kudi da su kayi kafa daga bankin.

Sahara Reporters ta fito da wata tattaunawa da aka yi tsakanin gwamnan na CBN, Godwin Emefiele, da wani mataimakinsa Edward Adamu, da kuma wani mai ba gwamnan babban bankin shawara mai suna Mista Emmanuel Ukeje.

Bankin ya fito ya tabbatar da cewa babu shakka, sakon sautin da aka ji yana yawo a gari, na gaskiya ne ba kage ba. Amma bankin ya bayyana cewa an zabi wasu tattaunawa ne da aka yi tsakanin gwamnan bankin da Abokan aikinsa.

KU KARANTA: Yadda za ayi bikin zarcewar Buhari a kan mulki a Najeriya

A jawabin dai an ji yadda gwamnan yake bayani a kan wasu makudan kudi na masu zuba hannun-jari da su ka lalace a bankin. A wannan sauti da aka bankado, an ji Emefiele yana maganar yadda zai samo kudi ya fanshe daga gwamnati.

Okorafor da yake karin bayani yace CBN ya cire makudan kudi domin taimakawa wasu jihohi a 2015, an yi hakan ne domin bada bashi ga ‘yan kasuwa saboda tattalin arzikin Najeriya ya farfado daga cikin wani hali na ha’ula’i inji CBN.

Kakakin na CBN yake cewa an bincike duk wasu akawun na CBN kuma an tabbatar da cewa sam babu wata badakala da aka tafka. Sai dai a wayar da aka ji gwamnan bankin yayi, an ji yana kuka da irin halin matsalar da ya samu kansa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel