Dalilin da yasa Buhari bai sanya baki a rigimar masarautar Kano ba

Dalilin da yasa Buhari bai sanya baki a rigimar masarautar Kano ba

Kungiyar labaran Buhari ta bayyana cewa bita da kullin siyasa ne ga duk wanda zai yi has ashen cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari na sane da shirin gwamnatin jihar Kano na kwace iko daga Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ta hanyar kafa sabbin masarautu.

Kungiyar ta BMO, a jawabin da ta saki a ranar Litinin, 13 ga watan Mayu dauke da sa hannun shugabanta, Mista Niyi Akinsiju da sakatarenta Mista Cassidy Madueke, tace babu adalci idan har wata jam’iyyar siyasa, kungiya ko wani yace da Shugaban kasa ya sanya baki a lamarin wanda karara yake lamari na jiha ne.

Kungiyar tace “Hasashen cewa da shugaba Buhari ya sani ya sanya baki a lamarin ba daidai bane kuma hakan rashin adalci ne domin kundin tsarin mulki bata ba Shugaban kasar ikon sanya baki a tsarin ba saboda lamari ne wata jiha.

Dalilin da yasa Buhari bai sanya baki a rigimar masarautar Kano ba

Dalilin da yasa Buhari bai sanya baki a rigimar masarautar Kano ba
Source: UGC

“Abu ne na cikin gida da ya shafi gwamnatin jihar Kano ba wai gwamnatin tarayya ba kuma ko Shugaban kasa bashi da karfi akai."

KU KARANTA KUMA: Sabbin Sarakuna: Mahaifin sanata Kwankwaso ya yi biyayya ga umarnin Ganduje

Kungiyar ta kuma jadadda cewa kundin tsarin mulki ta fayyace karfi Shugaban kasa ke dashi da kuma wanda gwamnonin jiha ke dashi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel